Assalamu alaikum Edita don Allah don Allah ka ba ni dama don in yi kira ga Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo (Talban Gombe) don ya sanar da mu inda aka kwana a kan alkawarin da ka yi na yi mana hanyar da ta tashi daga Jigawa da ke karamar Hukumar Nafada zuwa Ngalda da ke karamar Hukumar Fika.
Wannan alkawarin dai ka dauke shi ne a lokacin da kake yakin neman zabe a shekarar 2015 kuma har an fara aikin wannan hanyar kamar da gaske amma daga baya da aka lashe zaben 2015, sai aka tsayar da aikin hanyar aka dauke motoci da kayayyakin aikin hanyar aka tafi da su, abin ya zama ko kasa ko sama.
Wallahi rashin wannan hanya ba karamin ci baya ba ne ga karamar Hukumar Nafada a fannin kasuwanci. Hausawa kan ce in maye ya manta, uwar ’ya ba za ta manta ba, kuma don tuwon gobe ake wanke tukunya. Allah Ya ba mu shugabannin nagari masu kishinmu, amin summa amin.
Babangida Yusuf Nafada, Jihar Gombe, 08084618579