Bayan gaisuwa mai yawa a gare ku baki daya, ina fata ku Tashar Talabijin ta Arewa 24 da masu shirya shirin Dadin Kowa Sabon Salo kuna nan cikin koshin lafiya.
Bayan haka, zan yi amfani da wannan wasika tawa domin isar da sakon rashin jin dadin masoyanku da yawa, ciki har da ni kaina sakamakon shirinku kashi na 82 da kuka gabatar a makon shekaranjiya.
Rashin jin dadin da mu masoyanku muka ji shi ne, a kan rawar da Aminu Muhammad (Kawu Mala) ya taka a cikin shirin. Tun lokacin da kuka gabatar mana da Kawu Mala a cikin shirin Dadin Kowa Sabon Salo, kun nuna wa duniya cewa, shi mutumin arziki ne, wanda yake da rikon gaskiya, amana da kuma kawaici. Haka yana da tsayuwa ka’in da na’in a kan aikinsa, ba ya karbar cin hanci da rashawa sannan yana kokarin tsayawa sosai a kan ya ga ya magance duk wata matsala ta ma’aikatansu.
Amma kash, sai ga shi abin takaici da ban haushi da damuwa da kuka sa mana a cikin zukatanmu, ganin rawar da kuka ba shi ya taka ta satar na’urar taransfoma a Ma’aikatar Lantarki da yake aiki. A gaskiya wannan abu bai yi mana dadi ko kadan ba.
Wakakila a hasashena kuna son ku nuna mana cewa, Ma’aikatar Wutar Lantarki da Kawu Mala ke aiki a ciki ta daure shi ko ta kore shi saboda wannan abin kunya. Kuma hakan ya nuna mana illar shaye-shayen da Bintu ke yi wanda bai tsaya a kanta ita kadai ba har ta kai ga ya haifar da babbar matsala ga mahaifanta.
Duk da cewa shaye-shayen da Bintu ke yi su ne suka janyo masa shiga halin damuwar da yake ciki amma bai kamata ya tsinci kansa a sata ba, in muka duba hanyoyin nan guda bakwai:
1-Kada ku manta cewa matarsa (Yana) wato Salamatu Usman Goni, ma’aikaciyar asibiti ce kuma a hasashen mutane kowa ya san ma’aikatan asibiti suna da albashi mai dan tsoka. Duk da kun nuna zubin adashe take yi har ma ta dauki nata zubin ta tura wa ’yan uwanta domin a saya wa kanwarta kayan daki amma hakan ba zai sa ta kasa ajiye wani abu daga cikin albashinta saboda magance abin da ka iya zuwa bagatatan ba, tunda ba ita ke ciyar da gidan ba.
2-Kawar Yana (Likita) ita ma ma’aikaciyar asibiti ce har ma tana da gidauniyar tallafa wa mutane a kan harkar ilimi. Me ya sa ba ku umarci Yana ta kai kukanta wurin kawarta ba, duk da dai ita likitan ta fara sanin halin da Bintu ke ciki, da ta taimaka musu tunda komai nasu tare suke yi, ma’ana su aminan juna ne sosai?
3-Duk da Hashim Yarima (Ibrahim IB) ya ba da gudunmawar Naira dubu 20 don a yi wa Bintu aiki amma a wani shirinku na baya da kuka gabatar kun nuna shi (Ibrahim IB) sun gina makaranta kyauta sun mika ta ga Mato Yakubu (Malam Nata’ala). Shin me zai hana Ibrahim IB ya nemi tallafi daga wannan kungiya tasu tunda Kawu Mala ya sanar da shi yawan kudin da za a yi wa Bintu aiki?
4-Kawu Mala ma’aikacin wutar lantarki ne, me ya hana ku juya akalarsa ya tafi banki ya ci bashi a yi wa Bintu aiki da kudin?
5-Duk da yake ba ku nuna mana yadda hukumar gudanarwar ma’aikatar da Kawu Mala ke aiki ba amma mu a zatonmu suna jin dadin aikin da yake gudanar musu. In haka ne, me ya sa bai kai kukansa ga ita hukumar gudanarwar ko aro ne su taimaka masa da shi ba?
6-Shirin Dadin Kowa Sabon Salo kashi na 54, kun nuna mana wani Alhaji mai tausayi da son taimaka wa, wanda ba ya da shi (wanda ya taimaka da baro aka bai wa Abubakar B. Yola wanda aka sani da Dan Asabe dan gidan Ayuba Maigadi) shin me ya sa ba ku yi tunanin tura Kawu Mala wurinsa don ya ara masa kudin ba, sai dai kawai mu ga kun tura shi ya je ya saci taransforma?
7-Duk da talaucin da Kamaye yake fama da shi, bai taba tunanin ya je ya yi sata ba amma me ya sa sai a kan Kawu Mala?
A karshe, a matsayina na masoyinku, ina ganin tun da kun nuna mana Kawu Mala yana da tawakkali da kuma daukar kowace irin kaddara, ya kamata a ce kun tafi da shi a haka don nuna wa masu kallonku cewa duk abin da ya samu mutum, to daga Allah ne.
Ina fatan za ku wanke Kawu Mala daga wannan hali da ya shiga don ganin cewa mu masu kallo mun samu natsuwa, tunda kun nuna mana cewa saboda mu kuke yin shirin.