✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boris Becker ya yi asarar Naira Biliyan 41 a Najeriya

Zakaran qwallon Tenis na duniya kuma haifaffen Jamus Boris Becker rahotanni sun nuna ya yi asarar Fam Miliyan 100 kwatankwacin Naira Biliyan 41 a wasu…

Zakaran qwallon Tenis na duniya kuma haifaffen Jamus Boris Becker rahotanni sun nuna ya yi asarar Fam Miliyan 100 kwatankwacin Naira Biliyan 41 a wasu hannayen jari da ya saya a wani kamfanin da ke harkar man fetur a Najeriya.  Kamfanin wanda yake haxin gwiwa ne a tsakanin Kanada da Najeriya, rahoton bai bayyana suna ko a Jihar da yake da matsuguni ba.

Boris Becker wanda a bara ne wata kotu da ke Jamus ta wanke shi daga zargin qin biyan haraji a qasar yanzu za a iya cewa ya sake faxawa cikin tashin hankali ne bayan ya sake yin asarar kuxinsa a jarin da ya zuba a Najeriya.

Kamar yadda wani rahoto daga qasar Jamus ya nuna Boris dai ya zuba jarin Fam Miliyan 100 ne tun a watan Yulin 2013 a wani kamfanin mai a Najeriya kuma kamfanin haxin gwiwa ne a tsakanin wani kamfani da ke Kanada da kuma na Najeriya amma sai hannayen jarin suka yi qasa a kasuwar sayar da hannun jari (Stock Exchange).

A watan jiya ne dai Hukumar Kula da Hada-Hadar Hannayen Jarin ta tabbatar da durqushewar kamfanin da Boris Beckcr ya zuba jari a cikinsa, al’amarin da ta sa Becker da ire-irensa suka yi asarar Biliyoyin Naira.

Xan shekara 40 Becker ya tava zama zakaran tenis ta duniya bayan ya lashe Gasar Tenis ta Wembledon ta Ingila kuma ita ce mafi shahara a duniya.

Becker dai ya fara shiga matsala ne a shekarun baya tun bayan da ya kasa biyan bashin da ya ciwo a wani banki da ke Ingila da hakan ta sa bankin ya sayar da kadarorinsa a ke Jamus da sassan duniya. Sai ga shi a yanzu ya sake shiga mayuwacin hali bayan hannayen jarin da ya zuba a wani kamfanin mai a Najeriya sun narke.