Celso Borges dan kasar Costa Rica da ke buga wasa a kulob din AIK a kasar Sweden ya karbi aron riga a wurin dan kallo ya buga wasa.
Tun da farko ba a kawo rigar Borges ba, saboda ana tsammanin zai canza sheka zuwa kulob din Ebian da ke Faransa, amma da yake dan gani kashenin kulob din AIK ne sai ya karbi aron rigar wani mai goyon bayan kulob dinsa mai suna Luis, ya buga wasa da kulob din IFK Gothenburg.
“Ina cikin farin ciki bayan an yi amfani da riga ta wajen buga wasa har kulob din da nake goyon baya ya yi nasara da ci 2-0.” Inji Luis.
Bayan an kammala wasan ne aka mayar wa Luis rigarsa.
Borges ya ce ba zai ce wannan shi ne wasansa na karshe a AIK ba, saboda har yanzu ba a kammala tattaunawa kan canza shekarsa zuwa Ebian ba.
Borges ya karbi aron riga a wurin dan kallo ya buga wasa
Celso Borges dan kasar Costa Rica da ke buga wasa a kulob din AIK a kasar Sweden ya karbi aron riga a wurin dan kallo…