✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bom Ɗin Boko Haram Ya Kashe mutane 19 A Teburin Mai Shayi A Borno

Mutane 19 sun mutu sakamakon harin bom ɗin Boko Haram a teburin wani mai shayi, inda jama'a suke tsaka da hira a yankin Konduga

Mutane akalla 19 ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin bom din ƙungiyar Boko Haram a teburin wani mai shayi a Jihar Borno.

A daren Laraba ne mayakan kungiyar suka tayar da bom din a teburin mai shayin da jama’a ke hira a garin Kawuri da ke Karamar Hukumar Konduga.

Wani jami’in gwamnatin jihar ya ce mutane da dama sun samu raunuka a sakamakon tashin bom dinnda misalin karfe 8.05 na dare.

Jami’in gwamnatin ya ce, hatta wadanda abin ya rutsa da su ba za su iya fadin hakikanin yadda abin ya auku ba.

Ya bayyana cewa, “Babu wanda zai ya cewa ga abin da ya faru, amma mun fi kyautata zaton dasa bom ɗin aka yi, ba harin ƙunar baƙin wake ba.

“Mun gano gawarwakin mutane 19, amma ba mu tantance yawan wadanda suka samu raunuka ba.

“An kai wadanda suka ji raunin asibiti a Maiduguri domin ba su kulawa.”

Kokarin wakilinmu ba samun tsokaci daga ɓangaren hukuma kan lamarin bai yi nasara ba.

Wakilinmu a Maiduguri ya kira kakakin ’yan sandan Jihar Borno, DSP Kenneth Daso, domim samun karin haske amma wayarsa ba ta shiga.

Harin ya auku ne kwanaki uku bayan kungiyar ta kai hari a wani ofishin ’yan sanda inda ta kashe wani dan sanda da wata mata, suka kona motoci biyu a garin Jakana da ke karamar hukumar.

Kimanin awa 24 bayan ya nakiyar da kungiyar ta dasa ta  tashe wani jami’in kudi a ma’aikatar ilmin jihar bayan motarsa ta taka bom din a kan babban titin

Yankin Kawuri na da nisan kilomita 50 daga garin Maiduguri a kan babbar hanyar Maiduguri -Konduga- Bama.

Nakiyar da motar jami’in ta taka ta kuma jikkata mutane da dama.