✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bom ya tashi a sansanin sojin Afghanistan

Ba a tantance adadin sojojin da tashin bom din ya ritsa da su ba.

Rahotanni daga kasar Afghanistan sun ce, mutane da dama sun mutu, haka ma gommai sun jikkata sakamakon tashin bom da aka samu a sansanin soji da ke Kabul, babban birnin kasar.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida na kasar, Abdul Nafy Takor wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi, ya ce ba a kai ga gano dalilin tashin bom din ba.

Jami’in ya ce tashin bom din ya ritsa da dakaru da dama inda ya kashe na kashewa, kana ya jikkata wasu.

Sai dai jami’an gwamnatin Taliban ba su yi wani karin haske kan lamarin ba duk da an bukaci hakan daga gare su.

Taliban ta yi ikirarin fannin tsaronta ya bunkasa tun bayan da mulkin kasar ya koma hanunta a Agustan 2021, amma duk da haka ba ta daina fuskantar hare-hare ba.