✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bom ya kashe sojoji uku tare da raunata wasu a Borno

Sojojin sun taka bom din ne yayin da suke rakiyar matafiya a hanyar Dikwa-Gomboru Ngala.

Rahotanni a ranar Litinin sun bayyana cewa sojoji uku sun rasu, bayan taka nakiyar da Boko Haram suka binne a kan hanyar Maiduguri zuwa Gomboru a Jihar Borno.

Dakarun Bataliya ta 3 da ke Ngala na rakiyar matafiya a kan hanyar Ngala zuwa Dikwa ne lokacin da suka taka nakiyar, wadda ta kashe uku daga cikinsu, wasu kuma suka ji rauni.

“Wasu sun rasu, sannan wasu sun ji rauni, sakamakon binne nakiya da aka yi a kan titin Dikwa zuwa Gomboru Ngala.

“Muna addu’ar Allah Ya jikan su, sannan muna mika ta’aziyyarmu ga iyalansu,” a cewar majiyarmu.

Har wa yau, wata majiya daga masu aikin ba da agaji a Jihar ta tabbatar da faruwa lamarin, inda ta ce sojoji sun rasu, wasu kuma sun samu raunuka.

Majiyarmu ta tsaro ta bayyana cewa uku daga cikin sojin rasu, sannan motarsu ta yi raga-raga.

Sai dai ya zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, Rundunar Sojin Najeriyua ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba.