✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bom ya kashe mutane 8, wasu dama sun jikkata a Borno

Akalla mutane takwas sun mutu wasu da dama sun jikkata sakamakon tashin bom a hanyar Ngala zuwa Dikwa da ke Jihar Borno.

Akalla mutane takwas ne ake fargabar sun mutu sakamakon fashewar wasu bama-bamai a kan hanyar Ngala zuwa Dikwa a Karamar Hukumar Ngala a Jihar Borno.

Rahotannin sun nuna cewar, mutane da dama sun samu raunuka a sakamakon tashin bom din a kauyen Kinewba a ranar Talata.

Wata majiyar tsaro ta ce “Akalla Mutane  8 ne ake fargabar sun mutu, ciki har da yara biyu, sannan wasu da dama sun samu munanan raunuka sakamakon fashewar nakiyoyin.”

Majiyar ta ce fashewar bom din ya yi kaca-kaca da wasu motocin biyu yaddda ba za a iya gyara su ba.

Wata babbar majiya ta jami’an farin kaya na  JTF ta ce motocin biyu kirar Isuzu da wata babbar mota ce suka taka bom din kuma ana fargabar kashe kusan dukkan fasinjojin ciki.

“Wadannan motocin dai sun bar garin Ngala da misalin karfe 9 na safe, yayin da lamarin ya faru a nisan kilomita 15,” in ji majiyar.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, tashin bama-baman ya faru ne a tazarar kilomita 15 daga Maiduguri, babban birnin jihar.