✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Koli za ta yanke hukuncin zaben Kano ranar Juma’a

Tun a watan Maris ɗin 2023 ne ake ta sa-toka-sa-katsi a kotu tsakanin Gwamna Abba da Gawuna.

Kotun Koli ta ayyana jibi Juma’a a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan shari’ar zaben gwamnan Jihar Kano.

Sakataren kungiyar lauyoyi na jam’iyyar NNPP, Barista Bashir Tudun Wuzirci ne ya tabbatar wa Aminiya hakan.

“Eh, an tabbatar da hakan a hukumance. Sun ce mu bayyana ranar Juma’a domin yanke hukunci.

“Sun kuma shaida mana cewa ana bukatar lauyoyin da za su halarci zaman kotun daga kowace jam’iyya kada su wuce biyu, saboda za su yanke hukunci bakwai ne a wannan ranar ta Juma’a,” in ji shi.

Tun a watan Maris ɗin 2023 ne ake ta sa-toka-sa-katsi a kotu tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP da kuma Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC kan kujerar gwamnan Jihar Kano.

A watan Satumba ne Abba Kabir Yusuf ya kalubalanci hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben da ta soke nasarar da ya samu, inda ya daukaka kara.

Sai dai rashin gamsuwa da hukuncin ya sanya Gwamna Yusuf ya garzaya kotun daukaka kara, inda ta kara tabbatar da hukuncin da kotun sauraron korafe-korafen zaben ta yanke, tana mai kafa hujjar cewa gwamnan ba dan jam’iyyar NNPP ba ne a lokacin zaben saboda haka bai cancanci tsayawa takara ba.