Bom ya kashe wani jagoran jami’an tsaron sa-kai na Civilian JTF, wasu biyar kuma sun samu munanan raunuka bayan sun taka bom a Jihar Borno.
Wani babban jami’in Civilian JTF, Mohammed Aliyu, ya ce kwamandan mai suna Ibrahim Maliya da abokan aikinsa sun taka nakiya ne a lokacin da suke gudanar da aiki a kauyen Maliya da ke gundumar Mandaragarau a Karamar Hukumar Biu ranar Laraba.
Ya bayyana cewa jagoran nasu da ya rasu, Ibrahim Maliya Saidu, jarumi ne wajen yaki da mayakan Boko Haram da ISWAP a lokuta daban-daban, kuma shi ne Sakataren rundunarsu a Karamar Hukumar Biu.
Aminiya ta gano cewa mutum biyar din da suka samu raunkuna suna kwance a halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai a wani asibitin da ake jinyar su a garin Biu.
“Ya taka bom din da Boko Haram ta dasa ne a Mandaragarau da ke Biu, tare da sauran abokanmu, ciki har da Dokta Suleiman Sykami. Sykami da sauransu da suka samu raunuka kuma suna samun sauki,” inji Maiva.