✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bollywood: Kareena Kapoor ta kusa haihuwa a karo na 2

Ana sa ran tauraruwar za ta yi jego na biyu na da dan lokaci.

Tauraruwar fina-finan Bollywood, Kareena Kapoor ta wallafa wasu hotunanta dauke da tsohon ciki a wajen motsa jiki.

Kareena Kapoor ta wallafa hotunan ne a shafinta na Instagram, inda ake sa ran nan da wani lokaci ita da mai gidanta Saif Ali Khan za su samu karuwa a karo na biyu.

A hotunan da ta wallafa a shafinta na ta an ganta cikin shiga kala biyu, kowanne a lokacin da take motsa jiki.

Kareena Kapoor, yayin da take motsa jiki

Yanzu haka dai dan Kareena na farko mai suna Taimur, ya kai shekara hudu da haihuwa, kuma nan da wani lokaci ana sa ran tauraruwar ta Bollywood za ta haifa masa kani.

Tauraruwar Bollywood Kareena Kapoor Khan a lokacin da take motsa jiki.

Kareena ta rubuta littafi, wanda ake sa ran za ta sake shi a kasuwa mai suna ‘Kareena Kapoor Khan’s Pregnancy Bible.’

Kareena Kapoor dauke da juna biyu a yayin da take motsa jiki

Ana sa ran littafin zai taimaka wa mata masu juna biyu game da yadda za su kula da kansu yayin da suke da ciki.

Kareena Kapoor dauke da juna biyu a yayin da take motsa jiki

Ana sa ran littafin zai taimaka wa mata masu juna biyu game da yadda za su kula da kansu yayin da suke da ciki.