✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bollywood: Akshay Kumar ya kamu da COVID-19

Fitaccen jarumi a masana’antar shirya fina-finai ta Bollywood, Akshay Kumar, ya kamu da cutar COVID-19. Jarumin ya sanar da kamuwa da cutar cikin wani sakon…

Fitaccen jarumi a masana’antar shirya fina-finai ta Bollywood, Akshay Kumar, ya kamu da cutar COVID-19.

Jarumin ya sanar da kamuwa da cutar cikin wani sakon bidiyo a shafinsa na twitter a ranar Lahadi.

“Ina son na yi amfani da wannan dama don sanar da jama’a an yi min gwajin COVID-19 da safiyar nan, kuma sakamakon ya nuna ina dauke da cutar.

“Na killace kaina a gida kamar yadda doka ta tanada, kuma ina bin shawarwarin masana kiwon lafiya kan yadda zan kula da kaina.

“Ina ba wa wadanda suka yi hulda da ni shawara da su je a yi musu gwaji kuma ina nan dawo wa ba da jimawa ba,” a cewar Kumar.

Jarumin ya yi fatan samun waraka da dawowa bakin aiki don kammala wasu shirye-shirye da ya sa a gaba.