Shugaba Kasa Muhammadu Buhari ya jinjina wa Anthony Joshua, dan Najeriya mai rike da kambun damben duniya bisa nasarar da ya yi kan abokin karawarsa Kubrat Pulev, ranar Asabar.
Mai bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkar Watsa Labarai, Femi Adesina, ya fitar a wata sanarwa mai taken: “Shugaba Buhari ya jinjinawa wa Anthony Joshua bisa nasarar da ya yi kan Pulev”, a ranar lahadi.
- ‘Yan bindiga sun sace tsohowa mai shekara 90 a Zamfara
- Deontay Wilder da Anthony Joshua za su fafata damben boksin na Naira biliyan 80
- Yadda Anthony Joshua ya yi gaisuwar ban-girma ga Buhari
“Shugaba Muhammadu Buhari ya yi murnar muhimmiyar nasarar da dan asalin kasar Najeriya, Anthony Joshua, ya yi kan Kubrat Pulev a ranar Asabar.
“Shugaban Kasa ya ce kare Kambun IBF, WBA, da WBO da Joshua ya yi, ya kayatar da masu kallon wasan damben musamman a Najeriya da kuma duniya baki daya”, inji Femi Adeshina.
Ya ce Buhari ya kuma tuna haduwarsu da dan damben duniyar a farkon shekara da ake ciki a London, ya kuma kwatanta Anthony Joshua da cewar natsattse mutum ne da ya samu tarbiya mai kyau, “zai kuma ci gaba da daukaka”.
“Shugaba Buhari na yi wa Joshua fatan alheri a duk burin da ya sa a gaba na fuskantar Tyson Fury, kuma addu’ar daukacin ’yan Najeriya tana tare da shi”.