Anthony Joshua dan asalin Najeriya ya zama zakaran damben boxing na duniya ajin masu nauyi a karo na biyu bayan ya doke Andy Ruiz Jr dan kasar Mexico a damben da ya ja hankalin duniya wanda aka gudanar jiya Asabar a kasar Saudiyya.
Anthony Joshua dan Birtaniya, amma asalin dan Najeriya ya karbo kambunsa na IBF, WBA da WBO da Ruiz ya doke shi watanni shida da suka gabata a New York.
An gudanar damben ne a Diriyah Arena a birnin Riyad na Saudiyya a gaban ‘yan kallo sama da 14,000.