✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram: Wannan wane irin salon yaki ne?

Kwamared Bishir Dauda (08165270879) Sabuwar Unguwa Katsina ne ya mamaye shafinmu na makon nan da sharhinsa kamar haka:A halin da muke ciki, za mu iya…

Kwamared Bishir Dauda (08165270879) Sabuwar Unguwa Katsina ne ya mamaye shafinmu na makon nan da sharhinsa kamar haka:
A halin da muke ciki, za mu iya cewa muna cikin yaki, sai dai wannan karon muna cikin yaki mai wuyar sha’ani, wato Yakin Sunkuru ko Sari-Ka-Noke. Irin wannan yaki shi ne ya fi yawa a wannan karni na 21 maimakon yake-yaken baya, kamar yakin duniya na daya da na biyu, yakin Koriya, yakin bietnam, yakin Gabas Ta Tsakiya, yakin Laberiya da na Saliyo, yakin basasar Najeriya da sauransu. Wadannan yake-yake ne na fito-na-fito. Amma yake-yaken wannan lokaci kamar yakin da yanzu haka ke faruwa a Pakistan, Afghanistan, Iraki da Najeriya, yaki ne na sunkuru mai wuyar sha’ani.
Wani abin takaici ga irin wannan yaki shi ne, mutum bai san da wa yake yakin ba. Misali, a Irak, shin yaki ne tsakanin sojojin kawance da gyauren magoya bayan Sadam Hussain ne ko kuwa yakin addini ne tsakanin Shi’a da Sunni, ko tsakanin masu tsattsauran ra’ayi da gwamnati? Ko kuwa yaki ne tsakanin ’yan koren Turawa da sauran al’ummar Iraki? Kazalika yakin da ake a Najeriya, shin yaki ne tsakanin wadanda ake ce wa ’yan Boko Haram da Gwamnati ne ko kuwa yaki ne tsakanin Gwamnatin Najeriya da al’ummar Arewacin kasar, ko kuwa yaki ne tsakanin sojojin kasar da mutanen Arewacin Najeriya? Abu ne mai matukar wuya farat daya mutum ya iya tantance shin wannan wane irin yaki ne kasata take ciki.
Wane irin yaki ne wanda fara-ren hula sun fi masu kayan sarki rasa rayukansu? Wane irin yaki ne wanda ake kashe dalibai ’yan makaranta? Lallai wannan kazamin yaki ne.
Da yawa mutanen da wannan abu bai shafa ba kai tsaye sun dauka ba yaki ake ba, amma ko manazarta sun san cewa lallai kasarmu tana cikin yaki. Alkalumman da kungiyoyi masu zaman kansu ke badawa, ya ishe mu mu sake nazari.
A daidai wannan mawuyacin hali da kasarmu take ciki, sai ga shi wasu na hura kaho, wasu na buga kugen yaki. Shin masu wannan dabi’ar wai ba su da imani ne, ko kuwa ba su da hankali ko kuwa maganar Jonathan ta tabbata na cewa wasu sun rasa duk wata siffa ta dan Adam, kamar tausayi, jinkai, tsoro, nadama da sauransu? Shin ba za a tausaya wa talakan kasar nan ya ji da tsadar kananzir, tsadar sufuri, tsadar muhalli ba? Shin da wace azaba ce za a takaita wa talakan kasar nan? A dake ka, a mare ka, a yi maka fyade sannan a hana ka kuka? Wasu na maganar a yi yaki, wasu na maganar a raba kasar? Wasu na maganar su dole a bar su su handame dukkan dukiyar kasar, wasu satar kudin gwamnati ce a gabansu, wasu gani suke satar da suke ta yi kadan saboda haka dole a bude har asusun ajiya na kasashen waje su kwashe, shi ba mai tausayin kasar da talakan kasar wadanda su ne ke da rinjaye ba? Idan har mai girma Lamidon Adamawa zai harzuka ya ce ba su tsoron a raba kasar domin su suna da Kamaru da Chadi, shin su wa ke nan za su tsawata a kasar? Ko kuwa yanzu kasar babu dattawa masu hangen nesa? An yi yakin basasa a Najeriya tsakanin 1967 zuwa 1970, inda aka mutane, har aka yi amfani da shawarar Cif Obafemi Awolowo na yin amfani da yunwa a matsayin makamin yaki. Masu nazarin tarihi sun nuna cewa daruruwan yara kanana suka mutu, mutuwar gilla, sakamakon wannan mummunan yaki.
A lokacin da ake tafka wannan rashin imani, kasar  Faransa ta zama kanwa uwar gami, inda ta dinga daure wa Ojukwu damara, daga karshe dan tawayen ya tsere zuwa Abidjan, inda suka ba shi mafaka, sojojin Gwamnatin Najeriya suka yi nasara. Daga nan Shugaban Mulkin Soja na lokacin, Janar Yakubu Gowon ya fito da shirin da ake ma take da ‘3Rs’ wato gyara barnar da yaki yai da sasanta ’yan kasa. Ya fito da shirin yi wa kasa hidima, inda ake tura ’yan Kudu su yi bautar kasa tsawon shekaru uku a Arewa, su kuma ’yan Arewa a tura su Kudu, duk don a kawar da zaman rashin amana da fargaba tskanin ’yan Najeriya. Sojojin da suka biyo baya, sun yi bakin kokari wajen tabbatar da kasar ba ta wargaje ba, ciki har da hana Manjo Oka aiwatar da bakar aniyarsa. Babangida ya soke zaben 12 ga Yuni, a cewarsa matakin da ya dauka ya yi ne bisa kishin kasa, to amma abin ya kara raba kawunan ’yan Najeriya, har sai lokacin da su Babangidan da kansu suka fito da Obasanjo daga gidan kason Yola su ka yi mai wanka, suka yi mai riga da wando suka dora wa ’yan Najeriya shi.
Farkon mulkin Obasanjo, an samu rikice-rikice na kisan ’yan Arewa, musamman a Kudu-Maso-Yammancin Najeriya. Shi kansa Obasanjo ya dinga yi wa Arewar bita da kulli, ta hanyar yi wa manyan sojojin da suka fito daga yankin ritaya, sayar da kadarori ga ’yan uwansa Yarabawa, korar ma’aikata da sauransu. A gab lokacin da yake son yin tazarce, ya yi amfani da bambance-bambamcen da ke tsakanin ’yan kasar amma bai ci nasara ba, daga bisani ya dora mana shugaba mara lafiya, yanzu ga halin da muke ciki.
Na dauka ’yan Najeriya za mu koyi darasi daga tarihi, mu guji assasa duk abin da zai ingiza kasarmu cikin wani sabon yakin raba kasa. Na dauka cewa za mu ba makiyan Najeriya kunya, wadanda suka yi hasashen rushewar kasar shekara mai zuwa. Na dauka cewa za mu kalli Amurka da Tarayyar Turai, mu fahimci cewa kasa mai karfi ita ce dunkulalliya mai fadin murabba’in kasa da dimbin mutane kamar Sin. Amma sam, har yanzu ba mu ankara ba. Har yanzu ba mu san abin da ke tattare da raba kasar ba. Mun dauka cewa raba kasa kamar rabon gado ne. Duk mun mance da abubuwan rashin imani da hankali da ke tattare da rabon kasa.
Wannan lokaci, kamata ya yi mu mayar da hankali a kan yaki da cin hanci da rashawa, me ya sa gwamnoni ke handame kudaden jihohinsu? Me ya sa ciyamomi da kansiloli da ’yan majalisar jiha da na tarayya ke hada baki suna yi wa talaka 419? Me ya sa yau malaman Kwalejin Ilimi da na Kimiyya da Fasaha suke yajin aiki? Me ya sa ba ruwan fanfo ba asibitoci ba aikin yi ba ingantaccen ilimi? Wadannan su ne ya kamata mu fi babatu da zare na mujiya a kai, ba abin da bai da alheri ba.