✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta yi wa mutum 45 yankan rago a Kala Balge

Sun yi wa manoma kisan gilla da adduna a gonakinsu a garin Rann ranar Lahadi

Akalla mutum 40 ne mayakan Boko Haram suka yi wa yankan rago tare da jikkata wasu da dama a yankin Rann na Karamar Hukumar Kala Balge ta Jihar Borno.

Mayakan sun ritsa manoman suna aiki a gona ne suka rika saran su da adduna, a cewar Zagazola Makama, Kwararre da Yaki da Tayar da Kayar Baya kuma mai fashin baki kan tsaro a Yankin Tafkin Chadi.

“Akalla manoma 45 ne aka yi musu kisan gilla, aka yi wa gawarawkin wadansu daga cikinsu gunduwa-guwnduwa, wasu kuma daure su aka yi, aka yi musu yankan rago.

“Ranar Litinin aka yi jana’izar mamatan, a yayin da mazauna yankin ke cewa har yanzu akwai sauran mutanen da ba a gani ba,” a cewar Zagazola.

Majiyar Aminiya ta ce mayakan na Boko Haram sun kai harin ne a kan babura suka yi ta yi wa fararen hulan yankan rago ne bayan sun yi musu kawanya a ranar Lahadi.

Majiyarmu ta tsaro ta ce mayakan kungiyar sun kashe ’yan bola-jari da dama, kuma tuni aka yi musu sutura bisa tsarin Musulunci a ranar Litinin.

A zantawarta da Sashen Hausa na BBC, ’Yar Majalisar Wakilai mai waklitar yankin, Honorabul Zainab Gimba, ta tabbatar da kazamin halin, sannan ta bukaci jami’an tsaro da su kara azama wajen kare rayuka da dukiyoyin fararen hula a yankin.

Zuwa lokacin hada wanna rahoto, ana ci gaba da neman gwawarwakin manoman da mayakna ka far musu a yankin Rann, hedikwatar Karamar Hukumar Kala-Balge da ke Arewa maso Gabashin Jihar Borno.