’Yan ta’addan Boko Haram sun yanka wasu karin masunta bakwai da suka fito daga jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara a tsibirin Sabuwar Kwata da ke gabar Tafkin Chadi.
An kashe su ne saboda shiga yankin ba bisa ka’ida ba da kuma bijire wa dokokin kungiyar kamar yadda wata kwakkwarar majiya ta tabbatar.
- ’Yar Ekweremadu na neman taimakon koda
- Yadda sojoji suka yi raga-raga da ’yan ta’adda a Dajin Sambisa
Majiyar ta ce mayakan Boko Haram ne suka kama masunta bakwai a tsibirin bayan da suka buya suka ci gaba da kamun kifi, sabanin umarnin da Boko Haram ta bayar na haramta sana’ar ta su a yankin tafkin.
“’Yan Boko Haram ne suka gano masunta a tsibirin Sabuwar Kwata wadanda suka yanka su saboda kamun kifi a yankin ba bisa ka’ida ba duk da cewa tun da farko sun ba da umarnin cewa duk masunta daga Najeriya su fice,” kamar yadda wani mutum Alti Bawa ya shaida wata kafar yada labarai.
A karshen watan da ya gabata ne kungiyar Boko Haram ta bukaci dukkan masunta daga Najeriya da su fice daga tsibiran da ke karkashin ikonta, sakamakon kama masu sayar da abinci na kungiyar da kuma wani mai safarar kudi a yankin Diffa da hukumomin Jamhuriyar Nijar suka yi.
Sai dai bayan sanarwar janyewar, daruruwan masunta suka fice daga tsibiran yayin da wasu da dama da suka tsaya a baya domin shanya su, ’yan ta’addan kuma suka yi musu yankan rago a Kwatar Kaoulaha kusa da Sabuwar Kwata, a cewar wasu mutane da dama a yankin.
Masuntan da aka kashe sun ki ficewa ne saboda kamun da Tafkin ya yi musu, inda suke samun isassun kudade don ciyar da iyalansu, inji wani mai kamun kifi Salele Kabir.
“Babu wani wuri a Najeriya da ke samar da irin kifin da tafkin Chadi ke samarwa kuma wasu daga cikinmu ba sa damuwa da yin kasada da rayukansu don ci gaba da zama a tsibirin duk da dokar da aka ba su, kamar yadda wadannan mutum bakwai din suka yi,” inji Kabir.
Yankin Arewa maso Gabashin Najeriya na fuskantar hare-haren ta’addanci na tsawon shekara 13 daga kungiyoyin masu da’awar jihadi wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 40,000 tare da raba kusan miliyan biyu da muhallansu.
Rikicin ya bazu zuwa kasashen Nijar da Chadi da Kamaru da ke makwabtaka da kasar, lamarin da ya kara karfafa rundunar sojan yankin don yakar masu ikirarin jihadin.
A shekarar 2014, kungiyar Boko Haram ta kwace tsibiran da ke Tafkin Chadi bayan munanan hare-hare, lamarin da ya tilasta wa masunta tserewa daga gidajensu.
Kungiyar Boko Haram wadda har yanzu ke rike da tsibiran da ke gabar tafkin na Nijar, sun kuma bai wa masunta damar shiga yankunansu, bayan ganin makudan kudaden da ISWAP ke samu daga kudaden shiga na kamun kifi.