Rahotanni daga Jihar Borno sun ce mahara da ake zargi mayakan Boko Haram ne sun yi wa wasu manoman shinkafa yankan rago a ranar Asabar.
Akalla manoma 40 ne mayakan suka yi wa dirar mikiya a gonaki, suka daddaure su, suna yankawa a kauyen Koshobe, da ke Zabarmari, Karamar Hukumar Jere.
- Budurwa ta yi wa mahaifiyarta gunduwa-gunduwa
- A cafke barayin jariri mai kwanaki 3 a Kaduna
- ’Yan bindiga sun sha da kyar a hanyar Kaduna-Abuja
“Mun gano gawarwaki 43 da ka yi wa yankan rago da wasu mutum shiga da aka yi wa munanan raunika”, inji wani shugaban kungiyar tsaron sa kai, Babakura Kolo, wanda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato.
Ya ce ci gaba da cewa: “Ko tantama babu [aikin] Boko Haram ne da ke addabar yankin suna kuma kai wa manoma hari”.
Wani dan sa kai, Ibrahim Liman, ya ce manoman da abin ya ritsa da su masu kwadago ne a gonakin shinkafa da suka zo daga Jihar Sakkwato domin yin aikatau.
“Manoma 60 ne aka dauka aikin girbin shinkafa a gonakin; an yi wa 43 yankan rago, shida kuma sun samu raunuka”, kamar yadda ya shaida wa AFP.
Ya ce ana zargin ragowar mutum takwas da ba a gani ba maharan sun yi garkuwa da su ne.
Wani mazauni da aka yi akin neman manoman da shi, Mala Bunu, ya ce an kai gawarwarkin kauyen Zabarmari, inda za a yi musu sallar jana’iza ranar Lahadi.
Rahoton kamfanin dillancin labaru na Reuters ya ce tuni jami’an tsaro suka fara bin sawun maharan.
Sai dai rahoton ya ambato majiyar ’yan sa kai da ’yan sanda suna cewa mutum 40 ne aka kashe.
Zuwa lokacin hada wanna rahoton, kakakin ’yan sanda a Jihar Borno, DSP Edet Okon ya ce rundunar ba ta samu rahoto ba tukuna; Gwamnatin Jihar Borno ma ba ta fitar da sanarwa ba.
Tun a watan Satumba jihar ta fara mayar da mutanen da suka yi gudun hijira zuwa garuruwansu, kuma tana shirin kammala hakan zuwa karshen 2020.
A watan Oktoba, Boko Haram ta kashe manoman rani 22 a wurare daban-daban a kusa da Maiduguri.
Kungiyoyin Boko Haram da ISWAP sun yawaita kai hari a kan masu saran itace, makiyaya, manoma da masunta bisa zargin su da yi wa sojoji da ’yan sa kai leken asiri.
Akalla mutum miliyan 2.7 ne hare-haren Boko Haram ta tilasta wa yin gudun hijira a sassan jihar Borno, inji Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.