✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Boko Haram ta yi garkuwa da mata 2 a Konduga —‘Yan sanda

Mayakan Boko Haram sun yi awon gaba da ’ya’yan mutumin a kauyen Mairari.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Borno, Abdu Umar, ya ce mayakan Boko Haram sun sace wasu mata biyu a kauyen Mairari da ke yankin Karamar Hukumar Konduga a jihar.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Maiduguri, babban birnin jihar inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar 7 ga Yuni.

Ya ce, “Wani mai suna Ari Mustapha daga kauyen Mairari a Konduga ya kawo karar wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun mamaye masa gida sannan suka kwashi ‘ya’yansa mata guda biyu.

“Ya ce yaran nasa, guda na da shekara 26 gudar kuma 30.

“Haka nan, ya ce ’yan bindigar sun hada da wasu shanunsa biyu da sauran kayayyaki suka yi awon gaba da su,” inji kwamishinan.

Jami’in ya kara da cewa, bayan da rahoton faruwar lamarin ya isa gare su, sun tura jami’ai don bin sawun ‘yan bindigar amma ba samu nasarar cin masu ba.

Ya ci gaba da cewa, rundunarsu za ta zurfafa bincike har sai ta gano tare da kubutar da wadanda lamarin ya shafa, kana ta sadar da su da ahalinsu.

Kazalika, Kwamishinan ya bukaci al’ummar yankin da su kai karar duk wani al’amari da ba su yarda da shi ba ga hukumar tsaro mafi kusa don daukar matakin da ya dace a kan kari.