✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Boko Haram ta yi garkuwa da Hakimi a Yobe

Mayakan sun yi awon gaba da Hakimin Maganna bayan sun yi awa bakwai suna barna

Mayakan kungiyar Boko Haram sun sace Hakimin Maganna, Alhaji Zannah Laisu Kaigama a wani hari da suka kai garin Geidam, Jihar Yobe, a ranar Laraba.

Maharan sun lalata kantuna tare da kona wasu gidaje, suka kuma sace kayan abinci da magunguna a garin.

“Sun far wa garin ne cikin motoci biyar kirar Hilux, suna harbi a iska lamarin da ya sa kowa ya arce domin tsira da rayuwarsa,” inji wani mazauna garin.

Majiyarmu ta ce harin ya sanya firgici a zukatan mutanen garin, kasancewarta mayakan sun kusa awa bakwai suna cin karen karensu ba babbaka ba tare da wata gagarumar turjiriya daga jami’an tsaro ba.

Shugaban Hukumar ba da Agaji ta Jihar Yobe (SEMA), Mohammed Goje, wanda ya ziyarci garin Geidam domin gane wa idonsa irin barnar da aka yi, ya ce abubuwa sun daidaita.

“Kantuna biyar, runfunan kasuwa hudu, da wani shagon kwano da gidan wani basarake a garin, duk an kone su kurmus.

“An kuma sace kaya a ofisoshin Babban Asibitin Geidan da dakin ajiye magunguna inda aka kwashe magunguna da sauran kayan aikin jinya,” inji shi.

Ya kara da cewa maharan sun kuma dauke wata motar jami’an tsaron garin, sai dai ba a samu asarar rai ba.

“Yayin da muke tir da wannan harin, addu’o’in jama’a da kuma kokarin jami’an tsaro sun taimaka wajen takaita barnar,” a cewar jami’in.

Neman mayar da hannun agogo baya

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya umarci Hukumar ta SEMA da ta samar da kayan tallafin gaggawa da mutanen da harin ya shafa.

A yayin ta’aziyyarsa game da harin, gwamnan ya bayyana damuwarsa, yana mai cewa “an kai harin ne a lokacin da aka samu ingantuwar tsaro da kwanciyar hankali a jihar.

“Ingantuwar tsaro da kuma taimakon da gwamnati ke bayarwa sun ba wa jama’a damar komawa ga harkokinsu na neman abun dogaronsu na yau da kullum.”

Ya kar da cewa harin ba zai sa gwamnatin jihar ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na sake gina wuren da Boko Haram ta lalata da kuma mayar da mutane garuruwansu da suka yi kaura daga gare su ba.