Mayakan Boko Haram sun yi garkuwa da wani alkakin babbar kotu, Mai Shari’a Mshelia, tare da matarsa da direbansa da kuma dogarinsa a Jihar Borno.
A ranar Litinin 24 ne mayakan Boko Haram suka tare alkalin da abokan tafiyarsa suka yi awon gaba da su a kan babbar hanyar Biu zuwa Damaturu.
Majiyoyin leken asiri sun shaidawa Zagazola Makama cewa Mai Shari’a Mshelia na tafiya ne a cikin motarsa, tare da rakiyar direbansa da jami’in tsaro da matarsa ne suka yi kicibus da ’yan mayakan Boko Haram a tsakanin Burutai da Buni-gari zuwa Damaturu.
Ganin motar ce gungun ’yan Boko Haram din suka fito daga cikin jeji dauke da makamansu, suka tare hanyar.
- Majalisar Zartaswa ta jingine batun ƙarin mafi ƙarancin albashi
- An kama shi da kokon kan mutum a makabarta
Majiyar ta ce direban motar alkali ya tsaya tare da yin kokarin karkatar da motar domin samun damar tserewa amma kafin hakan ta samu ’yan ta’addan sun cim masu inda suka wuce da su zuwa Dajin Sambisa.
Majiyar ta kara da cewar, har zuwa yanzu ba a kai ga gano su ba.