Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Borno, Abdulkarim Lawan, ya ce a halin yanzu, Boko Haram na rike da ikon yankunan kananan hukumomi biyu a jihar.
Abdulkarim Lawan ya nuna damuwarsa kan dawowar ayyukan Boko Haram, duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta dage cewa babu wani yanki a jihar da ya rage a hannun ’yan ta’addar.
- NAJERIYA A YAU: ’Yan Bindiga Sun Zafafa Hare-Hare Bayan Samuwar Mai A Bauchi
- ’Yan bindiga sun kashe ’yan kasuwa 4 a Katsina
Shugaban majalisar ya ce a halin da ake ciki, yankunan kananan hukumomin Guzamala da Kukawa a yankin Borno ta Arewa suna karkashin ikon ’yan ta’addar ne.
Lawan wanda shi ne wakilin Guzamala a Majalisar Dokokin jihar, ya yi wadannan banyan ga manema labarai ne a ranar Lahadi.
Ya yi kira ga sojoji da su kara himma tare da kwato yankunan da lamarin ya shafa daga Boko Haram don maido da zaman lafiya a cikinsu.