✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Boko Haram ta kone garin Kareto, ta kashe mutm 13 a Damboa

Maharan Boko Haram sun kai farmaki tare da kashe masu sana'ar saran itace a Borno.

Akalla masu saran itace 13 ne suka mutu, baya ga kone garin Kareto da ’yan Boko Haram suka yi a jihar Borno a karshen mako.

’Yan ta’addar sun kone garin Kareto ne a ranar Juma’a tare da kone wasu sabbin gidaje da gwamnatin jihar ta gina wa ’yan gudun hijira.

Bayanai sun nuna cewa harin ya faru biyo bayan shirye-shirye da jihar ke yi na mayar da wasu ’yan gudun hijira zuwa garin.

Garin Kareto da ke Karamar Hukumar Mobar a Jihar Borno, shi ne garin da gwamnan jihar na farko ya fito, Marigayi Mohammed Goni.

A wani labarin kuma, ana zargin ’yan Boko Haram da kashe masu saran itace 13 a garin Damboa a ranar Juma’a.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na safe a yankin Chafa da ke karamar hukumar.

Wani dan banga mai suna Abakar, ya shaida wa wakilinmu cewa, “Lamarin ya faru da yammacin ranar Juma’a, kuma an kawo gawar wanda suka rasun, tare da musu sallah a gidan Hakimi sannan aka binne su”.

Sai dai hare-haren da aka kai Kareto da Damboa ba a samu rahotonsu ba sai dai na wanda aka kai Zubarmari, inda ’yan Boko Haram suka kashe manoma 43.