Wasu maharan da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari garin Katarko da ke Karamar Hukumar Gujba ta Jihar Yobe.
Wani mazaunin yankin, Garga Modu, ya tabbatar wa Aminiya cewa maharan sun kona makarantar firamare da cibiyar kiwon lafiya da ke yankin a harin da suka mamaye garin da alfijir yayin da ake shirin yin Sallar Asuba.
- Ba ruwanmu da lallashin ’yan bindiga —El-Rufai
- An yi wa sojojin da Boko Haram ta kora a Marte afuwa
- An rufe makarantun Birnin Gwari bayan garkuwa da daliban firamare
- An kashe ’yan bindiga 9 tare da kame wasu a Jihar Neja
“Da muka ji karar harbe-harbe sai muka koma gidajenmu muka sanar da makwabtanmu kowa ya gudu domin tsira.
“Daga cikin dajin, da muka boye muka hangi wuta na cin makarantar, sai muka yi gaba, daga baya aka kira mu cewa sun tafi, sannan muka dawo muka samu sun cinna wa asibitin wuta.
“Mun kuma samu labarin cewa maharan sun nufi sansanin sojoji a yayin inda suka yi musayar wuta da su,” inji shi.
Babu labarin asarar rai daga bangaren mazauna; mun kuma kokarin samun bayani daga Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Operation Lafiya Dole da ke Damaturu, Laftanar Kennedy Anyanwu kan batun amma hakan ba ta samu ba.
Kwamishinan Kula da Ayyukan Jinkai na Jihar Yobe, Abubakar Iliya, ya ce ya ziyarci yankin don jajanta musu a madadin Gwamnatin Jihar, tare da tantance irin barnar da aka yi.