Sanatan Kudancin Borno, Ali Ndume, ya bayyana cewa a halin yanzu mayaƙan Boko Haram sun ƙwace yankunan ƙananan hukumomi uku a jihar.
Ndume ya bayyana cewa mayaƙan kungiyar sun kashe fararen hula sanda a 200 da sojoji 100 a sabbin hare-haren da suka kai a sassan jihar a baya-bayan nan.
A wata zantawar da aya yi da ’yan jarida a ƙarshen mako, ɗan Majalisar Dattawan ya ce mayaƙan Boko Haram sun kai hare-hare 252 a daga watan Nuwamban 2024 zuwa yanzu.
Ya bayyana damuwa game da dawowar munanan ayyukan kungiyar a jihar duk kuwa da kokarin da sojoji da sauran hukumomin tsaro ke yi domin murƙushe su.
- Abincin karnuka ya fi wanda ake ba mu —Fursunonin Najeriya
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar Borno
A sakamako haka ne ya ce sanatoci da ’yan majalisar wakilan Jihar Borno da Gwamna Babagana Zukum, suka yi zama da sojoji da sauran hukumomin tsaro domin shawo kan matsalar.
Da yake tsokaci kan dawowar hare-haren, Sanata Ndume ya ce, “Wannan abin damuwa ne, duk da cewa sojoji sun halaka ’yan ta’adda sama da 800, su kuma ’yan ta’addan su kashe sama da 500 a sakamakon rikicin ISWAP da Boko Haram.”
Ya ce, “daga watan Nuwambar 2024 zuwa yanzu sun kai hare-hare 252, sun kashe sojoji 100 da fararen hula 500. Yanzu haka kuma kananan hukumomi uku na Jihar Borno — Gudumbari, Maye da Abadam — na hannunsu,” haka zalika sun tarwatsa wasu sansanonin soji da ke wurin.