A halin yanzu cikin mutanen Kauyen Garka ya duri ruwa bayan wani hari da mayakan Boko Haram suka kai Kauyen Dabna da ke Karamar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa.
Mazauna Kauyen Garka, inda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya fito, suna cikin firgici bayan samun labarin kawo musu hari da mayakan Boko ke shirin yi.
- Buhari da Osinbajo sun sa wa Janar Farouk anini
- ’Yan bindiga sun harbe Shugaban kasar Haiti Jovenel Moise
Wannan lamari na zuwa ne bayan kisan gillar da ’yan ta’addan suka yi wa mutum 18 a kauyen Dabna da ke makwabtaka da su.
Aminiya ta samu cewa, lamarin ya faru da safiyar ranar Laraba, inda wani mazaunin kauyen ya ce jama’a da dama sun yi kaura zuwa wasu kauyukan da ke makwabtaka da su domin neman mafaka.
Wani da ya tsallake rijiya da ya baya, Hilda Joshua, ya ce baya ga wadanda aka kashe, mutane da dama sun jikkata yayin harin da mayakan suka kai.
Ya ce da kyar ya samu ya tsere zuwa cikin jeji amma akwai ’yan uwansa da dama da kuma makwabta da abin ya rista da su a kauyen.
Haka kuma, wata majiyar ta bayyana cewa, bayan mutanen da aka kashe a cikin kauyen, ya kuma riski gawarwakin mutum uku a cikin dajin Kwapre da ke kusa da su.
Wasu majiyoyin sun ce, wani jirgin yaki na dakarun soji ya rika kai-komo a sararin samaniyar kauyen domin mayar wa maharan martani.
Sai dai neman jin ta bakin Mai Magana da Yawun rundunar sojin yankin, Manjo Muhammad Haruna, ya ci tura, a yayin da wakilanmu ba su samu layin wayarsa ba a lokacin hada wannan rahoto.