Wasu mahara da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kashe wasu masu aikin gini biyu tare da yin garkuwa da mafarauta uku a gidan hakimin garin Kukaretra da ke Karamar Hukumar Damaturu a Jihar Yobe.
Basaraken ya ce ’yan ta’addan da suka kai hari da misalin karfe 3 na asubahin ranar Lahadin sun shafe awa guda suna harbe-harbe, suka kona gidan nasa na motarsa, sannan suka kashe wasu daga cikin bakin nasa, suka sace wasu, a gidan da kan titin zuwa Maiduguri.
Hakimin garin, Alhaji Lawan Babagana, ya shaida wa Aminiya ta wayar tarho cewa ’yan ta’addan “Da misalin karfe 3 na asubahin ranar Lahadi suka kawo farmaki wannan gari namu suka rika harbe-harbe, suka banka wa gidana wuta, suka kona motata kirar Peugeot 504, sannan suka lalata gida daya a garin.
“Mutane biyar ne a gidana, wadanda masaukin bakina ne; biyu daga cikinsu ma’aikatan gine-gine ne da Hukumar Raya Arewa maso Gabas ta kawo daga Adamawa, domin gina Kasuwar Kukareta.
- Yadda Talakawa Za Su Biya Karin Dalar Da Akan Yi Wa Masu Shigo Da Kaya Ta Kago
- Tsohon gwamnan Yobe, Bukar Abba, ya rasu a Saudiyya
“Kamar yadda kuka sani a matsayina na sarkin gargajiya, nakan karbi bakuncin mutanen da ke zuwa yankina; Wadannan yara mayakan Boko Haram ne, sun fito da wadannan ma’aikatan daga gidana, suka harbe su nan take.
“Akwai mafarauta guda uku, wadanda nake karbar bakunci a gidana, inda wadannan ’yan ta’adda suka daure, suka yi garkuwa da su a cikin motar ’yan banga da aka ajiye a gidana,” Inji shi.
“’Yan sanda sun kwashe ragowar ma’aikatan ginin tare da kai su asibitin kwararru da ke Damaturu don duba lafiyarsu,” in ji shi.