✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta kai hari ofishin ’yan sanda a Borno

Mayaƙan sun kashe wani ɗan sanda da wata mace ɗaya a yayin harin na ba-zata.

Ana fargabar cewa mayaƙan Boko Haram sun kai hari ofishin ‘yan sanda na Jakana da ke Ƙaramar Hukumar Konduga ta Jihar Borno.

Maharan sun kashe ɗan sanda ɗaya da wata mace a yayin harin da suka kai cikin duhun dare.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa maharan sun gudu da makaman ‘yan sandan sannan kuma sun ƙona motocin sintiri biyu da babur ɗaya.

Wakilinmu ya ruwaito cewa maharan sun kai harin ba-zata inda suka isa ofishin ‘yan sandan da misalin ƙarfe ɗaya na dare sannan suka yi ta musayar wuta da ‘yan sandan har zuwa uku na dare.

Majiyar ta bayyana cewa maharan sun yi galaba kan ‘yan sandan inda suka afka cikin ofishin nasu suka ƙona motocin sinitiri biyu wadda ɗaya ta ‘yan sanda ce ɗaya kuma ta ‘yan banga.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Konduga, Honarabul Abbas Ali Abari ya tabbatar wa ‘yan jarida kai wannan harin sai dai bai yi ƙarin bayani ba.

Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, Nahun Kenneth, sai dai bai amsa kira waya da saƙon kar ta kwana da aike masa ba.

Jakana na nan a kan babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri da ke da tazarar kilomita kimanin 45 tsakani da babban birnin na Jihar Borno.