✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Boko Haram ta kai sabon hari a garin Geidam

Mayakan Boko Haram sun kai sabon hari dab da bude-baki a garin Geidam ranar Juma’a.

Mayakan Boko Haram sun kai sabon hari a garin Geidam na Jihar Yobe, da Magaribar ranar Juma’a.

Mayakan a cikin motoci dauke da muggan makamai sun yi wa garin dirar mikiya ne tun da misalin karfe shida na yamma.

Mazauna garin sun shaida wa Aminiya ta wayar salula cewa, “Da shigan maharan garin, sai ayarin motocinsu ya zarce zuwa makarantar firamaren da ke Kafela suka fara barin wuta babu kakkautawa.

“A halin yanzu muna cikin gidajenmu muna addu’ar Allah Ya kare mu; Iya abin da zan iya cewa ke nan a yanzu.”

Kakakin ’yan sandan Jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da harin, tare da cewa tuni dakarun sojin sama suka isa garin domin kai dauki.

Sai dai ya ce babu karin bayani game da yawan mutanen da lamarin ya ritsa da su, a halin yanzu.