Ana fargabar mutane da dama sun riga mu gidan gaskiya yayin da gommai suka jikkata a sakamakon wani hari da mayakan Boko Haram suka kai Karamar Hukumar Askira Uba da ke Jihar Borno.
Bayanai sun ce mayakan sun kutsa kauyen Kilangal, mahaifar Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Injiniya Abdullahi Musa da tsakar ranar Lahadi, inda suka cinna wa gidaje wuta.
- Gwamnatin Habasha ta soma kwato garuruwa daga hannun ’yan tawaye
- Karancin dala: Sri Lanka za ta rufe ofishin jakadancinta a Najeriya
Majiyar rahoton ta ce wani jirgin yaki na dakarun sojin sama ya kai dauki kauyen sa’o’i biyu bayan aukuwar lamarin, sai dai tuni aikin gama ya gama.
A cewar majiyar, mayakan sun ci karensu babu babbaka a yayin da babu wata tirjiya da suka fuskanta, inda ake zargin cewa mutane da dama sun tsere cikin jeji yayin da kuma wasu karar kwana ta cimma su.
A watan jiya na Nuwamba ne mayakan kungiyar ISWAP masu ikirarin jihadi a yammacin Afirka suka ka yi dauki ba dadi da dakarun sojin Najeriya a Karamar Hukumar Askira Uba da ke Bornon.
Mayakan sun yi wa Askira/Uba dirar mikiya ne da misalin karfe bakwai na safiya a cikin jerin gwanon motoci da suka kai akalla 16, inda suka yi luguden wuta a yankin Ngude.