Rundunar ‘yan sandan Jihar Borno ta sanar da samun nasarar cire wani bam da mayakan Boko Haram suka binne a yankin Dalori da ke Karamar Hukumar Konduga a Jihar.
Aminiya ta gano cewar mutane sun ankara da bam din ne da misalin karfe 6:00 na safe, yayin da suka hangi wani abu boye a cikin buhu wanda ake zaton abun fashewa ne, lamarin da ya sa mazauna sansanin suka bar matsuguninsu, suka gudu Dalori da ke da nisan kilomita da hanyar Maiduguri zuwa Bama.
- Tsohon dan wasan Barcelona, Maxi Rolon ya mutu a hatsarin mota
- Fasinjojin Kamfanin Azman sun makale tsawon sa’o’i 24 a Kano
Da ya ke jawabi yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Maiduguri a ranar Litinin, Kwamishinan ‘yan sandan Jihar, CP Abdu Umar, ya ce nan take aka aike da jami’an rundunar ‘yan sandan da ke kula da bama-bamai zuwa wurin da abin ya faru domin kai dauki.
Kwamishinan ya bayyana cewa an kwashe kowa daga yankin gaba daya sannan ya shawarci mazauna yankin da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum bayan cire bam din.
Umar ya ce, “An gano wasu abubuwan fashewa ba a san ko su waye suka dasa a cikin bokitin roba kusa da sansanin ‘yan gudun hijira ba, amma an samu nasarar cire bam din ba tare da an samu asarar rayuka ba ko dukiya ba.”