✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Boko Haram: Shekau ya koka kan yawan hare-haren sojoji

Biyo bayan bullar wani sabon sako mai dauke da muryar da aka yi ittifaki ta shugaban Boko Haram ce, Abubakar Shekau alamu na nuna cewa…

Biyo bayan bullar wani sabon sako mai dauke da muryar da aka yi ittifaki ta shugaban Boko Haram ce, Abubakar Shekau alamu na nuna cewa kungiyar ‘yan tayar da kayar bayan tana kwasar kashinta a hannu.

A cikin sakon mai tsawon minti daya da sakon 22, an ji muryar  Shekau yana addu’ar Allah Ya kawo masa dauki shi da mabiyansa daga luguden wutar da rundunar sojojin Najeriya ke ci gaba da yi musu.

Shekau wanda ya yi magana a cikin harsunan Larabci da kuma Kanuri ya ce yawan hare-haren da sojoji ke kai musu a wannan wata na Ramadan ya sa suna shan wahala matuka.

Ba kasafai dai ake jin jagoran ‘yan tayar da kayar bayan yana magana a irin wannan yanayin ba, wanda hakan yasa masana harkar tsaro da dama ke ganin Boko Haram na cikin wani hali.

A ‘yan kwanakin nan dai rundunar sojan Najeria ta ce ta zafafa kai hare-hare kan ‘yan ta’addar.

Idan za’a iya tunawa, a kwanan nan Babban Hafsan sojin kasa na Najeria, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya sanar da tarewa a yankin Arewa Maso Gabas har sai sun ga bayan kungiyar ta Boko Haram.

Rikicin Boko Haram dai ya fi kamari a yankin Arewa maso Gabas kuma an shafe sama da shekara 10, ya kuma yi sanadiyyar rasa rayukan dubun mutane tare da raba sama da miliyan biyu da muhallansu.

%d bloggers like this: