✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram na shirin kutsawa cikin masu zanga-zanga —’Yan sanda

’Yan sanda sun yi gargadi cewa ‘yan Boko Haram na shirin kutsawa cikin zanga-zangar da za a fara a Jihar Yobe ka matsalar tsadra rayuwa

’Yan sanda a Jihar Yobe na zargin mayakan kungiyar Boko Haram na shirin shiga rigar masu zanga-zangar gama-gari a ake shirin gudanarwa daga ranar Alhamis.

Kakakin yan sandan jihar, DSP Dungus Ibdulkarin, ya sanar cewa sun samu rahotanni cewa, wasu da bai bayyana ba, sun dauko sojojin haya daga kasashen waje na shirin domin barnata rayuka da dukiyoyin jama’a a lokacin zanga-zangar da ke tafe.

Sanarwar da DSP Dungus Abdulkarim ya futar a ranar Asabar ta shawarci masu shirin shiga zanga-zangar da suka yi hattara, su kasance masu lura.

“A yayin da Jihar Yobe ke farfadowa daga tashe-tashen hankula, kwamishinan ’yan sanda, Garba Ahmed, ya amince da ’yancin ’yan kasa na gudanar da zanga-zangar lumana.

“Muna faɗakar da ’yan kasa cewa akwai masu wasu da mugun nufi, don haka hatta zanga-zangar lumana a wannan lokacin na iya zama bai dace ba.

“Fashewar bom da kuma harin ta’addancin baya-bayan nan a Karamar Hukumar Gujba sun haifar da damuwa.

“Ba ma son mu shiga karin kalubalen tsaro,” in ji sanarwar da rundunar ta fitar.

Jami’in ya kuma yi gargadin cewa masu aikata laifukan da ke kokarin fakewa da zanga-zangar don taya da zaune tsaye a jihar za su yaba wa aya zaki.

A cewar Abdulkarim, don gudanar da zanga-zangar ba tare da wata tangarda ba, akwai bukatar masu yi su sanar da hanyoyin da za su bi da wuraren da za su ga gudanar tarukansu da tsawon lokacin da za su dauka gami da sunaye da bayanan tuntubar shugabanninsu da kuma matakan da suka daunka na hana bata-gari shiga cikinsu.

“Ta hanyar samar da wadannan bayanai, za mu iya tura isassun ma’aikata da kayan aiki

“Muna rokon masu zanga-zangar su ba ’yan sanda hadin kai, da biyayya ga doka, da kuma nuna kyawawan halaye don yin taron cikin lumana.

“Mun kuduri aniyar yin aiki tare da kowa don samar da tattaunawa da samun zaman lafiya mai dorewa,” in ji rundunar.