Mahukuntan Tsaro a Najeriya sun yi ikirarin cewa, kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram, na shirin kai hari Abuja, babban birnin Kasar da kuma Jos, babban birnin Jihar Filato.
Mukaddashin Babban Sufeton ’Yan sandan Najeriya, Usman Baba ne ya bayar da wannan sanarwa ta ankarar da jami’an tsaro tare da neman su tashi su farga kan halin da ake ciki.
- Ta auri maza bakwai don samun haihuwa da kowanensu
- A Morocco za a yi wasan karshe na kofin zakarun nahiyyar Afirka
Sanarwar hakan na kunshe cikin wata takarda mai kwanan watan 19 ga Mayun 2021 dauke da sa hannun wani babban jami’i, Idowu Owohunwa wacce aka aike wa Kwamishinonin ’Yan sandan biyu.
Da wannan ne Mukaddashin Babban Sufeton ’Yan sandan yake kira ga dukkanin Kwamishinonin ’Yan sanda a wuraren biyu da su kasance cikin shirin ko ta kwana, yana mai cewa bayanan sirri sun tabbatar musu da cewa ’yan ta’adda na ci gaba da kulla dabarun a kan kudirinsu.
A cewarsa, Muhammad Sani, wani Kwamandan Boko Haram da ke zaune a Dajin Sambisa tare da mataimakinsa, Suleiman da ke Gashua a Jihar Yobe, za su hada kai wajen jagorantar kai hare-haren.
A takardar mai lamba TB:0900/IGP.SEC/ABJ/VOL.TI/47, Mukaddashin Babban Sufeton ’Yan sandan ya umarci Kwamishinonin ’Yan sandan biyu da su yi bitar tsare-tsarensu tare da karfafa tsaro a wuraren da gine-ginen Gwamnnati suke a Abuja da Jos.
Aminiya ta ruwaito cewa, wannan ankararwa da Mukaddashin Sufeton ’Yan sandan ya yi na zuwa ne makonni bayan da Gwamna Abubakar Sani Bello na Jihar Neja ya yi ikirarin cewa babu sauran aminci kuma birnin Abuja ba zai zauna lafiya ba a yayin da Mayakan Boko Haram suka kafa tutarsu a wasu yankunan jiharsa.