Kungiyar Boko Haram ta nemi a biya ta Dala dubu dari biyar a matsayin kudin fansa kafin ta saki wasu ma’aikatan agaji hudu da wani jami’in tsaro da mayakanta suka kama.
Mayakan Boko Haram na bangaren Albarnawi (ISWAP) sun nemi a biya su kudin ne ta wani bidiyo da suka fitar wanda a cikin mutaten da kungiyar ta kama suke rokon gwamnatin Najeriya da kungiyoyin agajin su cece su.
- Boko Haram ta saki bidiyon mutanen da ta kama suna neman dauki
- Jirgin soji ya ragargaji kwamandojin Boko Haram a Borno
Mutanen sun hada da mutum daya-daya daga kungiyoyin agaji na Action Against Hunger da Reach International da International Rescue Commitee da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta jihar Borno (SEMA). Na biyar dinsu wani jami’in tsaro ne mai zaman kansa.
Mutanen da bidiyon na ISWAP ya nuna suna rokon Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin su ceci rayuwarsu sun ce mayakan sun kama su ne a farkon watan Yuni a kan hanyar Maiduguri zuwa Monguno a jihar Borno.
Kungiyar agaji ta Action Against Hunger wadda a bara ma ‘yan Boko Haram sun yi garkuwa da wasu ma’aikatanta guda shida ta tabbatar da cewa an kama mutanen ne tun a watan jiya.
Wannan na daga cikin ‘yan lokuta kalilan da kuniygar ke fitowa karara tana neman kudin fansa kafin ta saki wadanda ta kama, amma wasu masu sharhi na ganin babu tabbas ko Gwamnatin Najeriya za ta yi abin da mayakan ke nema.
Suna kafa hujja da cewa gwamnatin na iya yin taka-tsantsan game da hakan, domin biyan kudin fansar na iya ba wa mayakan kwarin gwiwa a matsayin wata tabara na tayar da tattalin arizikinta da kuma takura wa gwamnatin.