✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Boko Haram: Mun kosa mu koma bakin daga —Sojojin da suka ji rauni

Wasu sojojin Najeriya da suka jikkata yayin gwabza yaki da mayakan Boko Haram sun sha alwashin komawa fagen daga har sai a ga bayan kungiyar.…

Wasu sojojin Najeriya da suka jikkata yayin gwabza yaki da mayakan Boko Haram sun sha alwashin komawa fagen daga har sai a ga bayan kungiyar.

Sojojin sun yi alkawarin ne lokacin da Shugaban Kwamitin Rundunar Sojin Kasa a Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume ya je domin duba su a Asibitin Sojoji da ke Maiduguri ranar Lahadi.

Daya daga cikin sojojin Kofur Abubakar Bukar, wanda ya samu raunin harsasai a lokacin da mayakan suka kai musu hari a hanyar Damboa a watan Disamban 2020, ya ce a shirye yake ya koma fagen daga don shiga cikin takwarorinsa a ci gaba da ragargazar ‘yan ta’addan.

“Ina gode wa Allah da Ya tseratar da ni daga harin. Amma a matsayina na soja, a shirye nake na koma cikin abokan aikina don ci gaba da fada har sai mun kubatar da kasarmu ,”inji shi.

Shi ma Kofur Kolawole Omosheye, wanda yake jinyar raunin harsashin da ya samu bayan mahara sun far masu a Tunkushe inda suka gwabza na sama da tsawon lokaci ya ce a shirye yake ya koma fagen daga.

“Ina samun sauki kuma cikin makonni biyu masu zuwa, zan koma inda nake aiki. Muna godiya ga Allah da kuma GOC wadanda suka zo tare don karfafawa mana gwiwa”, inji sojan.

Wani kurtun soja, Saidu Dahiru wanda bangorin bom ya doke shi ya ce, “ina samun sauki kuma nan da makonni biyu masu zuwa, zan koma don ci gaba da gwagwarmaya.”

Shi ma Ademola Felix, ya sha alwashin mayar da martani ga masu tayar da kayar bayan, idan ya koma sansaninsa da ke Gamborun Ngala.

Felix ya ce ya ji rauni ne lokacin da motocinsu suka taka nakiya, wanda ya kashe abokan aikinsa, yana mai cewa “ina so in koma in ba su kashi sosai.”

A jawabinsa, Ndume ya ce ziyarar kokarin karfafa gwiwar sojojin da suka samu rauni ne a sassa daban-daban na yankin Arewa maso Gabas.

Ya ce wannan shawarar ta kuma biyo bayan rahotannin da wasu kafafen yada labarai na baya-bayan nan da ke zargin an yi watsi da sojojin da suka jikkata.

Ndume ya ce irin wadannan labarai na iya karya gwiwar sojojin da ke sadaukar da rayukansu don ceto kasar.

“Mun ziyarci dukkannnin sassan asibitin kuma kulawar da aka ba ma’aikatan abin a yaba ne.

Da muka muka zo, an gaya mana cewa masu bukatar karin kulawa an kwashe su zuwa Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna, daya daga cikin asibitoci mafiya inganci a kasar nan.

Najeriya kasarmu ce dukkanmu, alhakinmu ne mu karfafa gwiwar sojojinmu masu fada da kuma tallafa musu da dukkan abin da suke bukata

“Ina tabbatar wa marasa lafiyan da hafsoshin soji cewa dukkanmu ’yan Najeriya muna bayansu, kada ku karaya. Su ci gaba da aiki, domin wannan abin da kuke yi ba wai na kasa kawai ba ne, aiki ne na Allah.

“Allah zai sāka muku saboda sadaukarwar da kuka yi kuma Kwamiti da Majalisar Tarayya za su ci gaba da mara muku baya”, inji Ndume.

Ya kuma yaba wa Babban Kwamandan Runduna ta 7, Manjo.-Janar Abdul Khalifa, saboda jajircewarsa da ya samar da nasarorin da aka samu.

“Kishin kasar da kuka nuna da kuma sadaukarwarku shi ne abin da ya ratsa sojojin, muna rokon Allah Ya kara yi muku jagora a samu biyan bukata”inji shi.

Manjo-Janar Khalifa ya yi alkawarin cewa Runduar za ta ci gaba da ba da muhimmiyar kulawa ga jin dadin dukkannin sojoji.

“Kun zagaya kun gani da kanku sannan kuma kun yi hulda da sojojin da suka samu rauni.

“Za mu ci gaba da yin iya kokarinmu don ganin an kula da su yadda ya kamata,” inji shi.

%d bloggers like this: