Bayanan da ke fitowa daga garin Dapchi na jihar Yobe zuwa yanzu sun nuna cewa gidan dagaci da wani dakin shan magani aka kona a wani hari da wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan Boko Haram ne suka kai da maraicen Litinin.
Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun yi wa garin kawanya ne da misalin karfi 5:30 na yamma, kuma suka yi nasarar balle shaguna da dama suka debi kayan abinci masu tarin yawa, a yayin da al’ummar garin ke dab da bude baki saboda azumin watan Ramadan.
Wata majiya a garin na Dapchi ta tabbatar wa Aminiya cewa lokacin da maharan suka dirar wa garin babu sojoji a ciki, hakan kuma ya sa suka ci karensu ba babbaka.
Majiyar ta kara da cewa ko da yake daga bisani ’yan sanda sun yi nasarar korar maharan da kashe wasu daga ciki, ’yan bindigar sun kona gidan dagacin garin da wani asibitin shan magani.
Hakazalika, rahotanni sun tabbatar da cewa da misalin karfe 8:00 na dare sojoji suka shiga garin inda suka fatattaki maharan.
Yawan asara
To sai dai zuwa yanzu Aminiya ba ta iya tantance hakikanin asarar da mutanen garin suka yi ba saboda rashin kyawun layin sadarwa.
Haka ma yunkurin jin ta-bakin rundunar sojin Najeriya bai yi nasara ba saboda mai magana da yawun rundunar a yankin, C. P. Oteh, bai amsa kira ko rubutaccen sakon da muka tura masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Galibi dai a irin wadannan hare-hare, ’yan ta’addar kan fi mayar da hankali ne wajen fada da jami’an tsaro tare da kokarin dibar kayan abinci daga shagunan mutanen gari.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar 19 ga watan Fabrairun 2018 ne dai mayakan Boko Haram suka sace ’yan mata 110 daga Kwalejin Kimiyya ta ’Yanmata da ke Dapchi.
A watan Maris din 2018 aka saki dukkan ’yanmatan, ban da Leah Sharibu, wacce ita kadai ce Kirista a cikinsu.