Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya ba da sanarwar tallafin Naira miliyan 23.5 ga iyalan sojojin nan 47 da suka rasa rayukansu a wani harin kwanton bauna da ‘yan Boko Haram suka kai musu a ranar Lahadin da ta gabata a jihar Yobe.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a lokacin da yake jawabi ga iyalan sojojin a barikin Maimalari da ke Maiduguri.
A cewar Gwamna Zulum, kowanne iyali zai samu tallafin Naira 500,000.
Sai dai ya ce hakan ba ya nufin kudin diyya aka ba su illa dai an yi hakan ne kawai don rage musu radadin da suke ciki, duba da halin da tattalin arzikin kasar nan ya shiga a dalilin bullar cutar Murar Mashako (COVID-19).
“Ku da kuka rasa mazajenku da ma masu auren da suke da yara, ku sani muna tare da ku, a sane muke da irin gudunmawar da mazajenku suke bayarwa, muna tare da ku a kowanne hali, kuma muna jinjinawa mazajenku”, inji Gwamnan.
Ya kuma ba da umarnin samar da sahihi kuma ingantattacen jadawalin sunayen matan da lambar asusun ajiyar bankinsu da kuma sana’ar da suke bukatar yi, don a tura musu abin tallafi da za su fara sana’a.
Babban Kwamandan Runduna ta 7 ta Sojin Kasa mai mazauni a Maiduguri, Birgediya Janar A.K. Ibrahim, shi ne ya karbi Gwamna Zulum, wanda ya shaida masa cewar, “Mun zo ne domin mika sakon ta’aziyar Gwamnati da al’ummar Jihar Borno a kan wannan rashi na zaratan sojojinmu wadanda suka rasa rayukansu a makon jiya”.