Gwamnatin Jihar Neja ta ayyana takunkumi gudanar da wa’azi tare da rufe makarantu da ke da nasaba da wani malami, kan zargin sa da yaɗa aƙidu irin na ’yan Boko Haram.
Matakin, kamar yadda daraktan kula da al’amuran addini a jihar, malam Umar Faruk, ya shaida wa Aminiya, ya biyo bayan tattaunawar da ta gudana ne a tsakanin malamin da kuma hukumar a ranar Litinin 18 ga wannan watan, inda bayanansa suka tabbatar da abin da a ke zarginsa da shi.
Ya ce makarantun da malamin ke jagoranta da ke ƙarƙashin masarautar Suleja da a ka fi sani da suna Markaz Ummina Habiba da ya haɗa da na yara da kuma manya za su ci gaba da kasancewa a garƙame har sai bayan samun sakamakon bincike na jami’an tsaro kan lamarin.
Aminiya ta samu labarin cewa makarantun malamin sun haɗa da wani da ke unguwar bayan Neja Motel da ke garin Suleja da kuma wani da ke ƙauyen Gajiri da ke yankin Ƙaramar Hukumar Tafa, da ke ƙarƙashin masarautar ta Suleja.
- ’Yan ta’adda ke lalata da ’yan mata da sa su ƙunar baƙin wake —NCTC
- Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa
Daraktan ya ce gwamnatin jihar ba za ta zuba ido kan malamin ba da a ke zargi da bayanan tayar da husuma tare da cusa wa al’umma aƙidar ƙiyayya ga juna ba.
Ya ce hukumar ta samu fayafayan malamin daga ɓangarori daban-daban na yaɗa aƙidun da ya suka haramta yin zaɓe da kuma yin aikin gwamnati.
Jami’in ya ce ofishinsa zai rubuta takarda ga ƙananan hukumomin Gurarada Tafa da kuma Suleja kan matakin da a ka ɗaukan tare da neman su sa ido ga sauran masu aƙidu irin nasa, don xauƙan mataki a kansu.
“Za mu kuma rubuta takarda ga jami’an tsaro kan buƙatar gudanar da nasu bincike a kai tare da miƙa wa ga gwamnan jihar, wanda za a yi amfani da shi wajen ɗaukar mataki na qarshe, na kan a ba shi damar dawo da ayyukansa ko kuma a ci gaba da dakatar da shi.
“Mu dai a iya bincikenmu bayan zantawa da shi ya bayyana cewa aƙidojinsa irin na Boko Haram ne. Sai dai su jami’an tsaro tun da ƙwararru ne kan gudanar da bincike, rahotunsu ne zai kasance na ƙarshe,” in ji Daraktan.
A martanin da ya mayar, malamin mai suna Muhammad Bin Muhammad ya ce yana nan kan matsayarsa kan tsarin demokraɗiyya da a ke zaɓen shugabanni ya saɓa wa Musulunci saboda shirka ne na ɗaukan haƙƙin Allah ana bai wa wasu al’umma na su mulki kansu da kansu.”
Sai dai ya ce ba ya sukan yin karatun boko wanda yake ɗauka a matsayin tsani na yin sana’a inda ya ce shi kansa yana da shaidar karatun digiri na biyu da ya samu daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
A cewarsa matakin da hukuma ta ɗauka bai dace ba, inda ya ce kamata ya yi a kira taron muƙabala a tsakaninsa da sauran malamai da ke sukar aƙidarsa, don jin hujjojin kowanne daga cikinsu, inji shi.