Wasu shugabanni na Amurka sun gano yadda mayakan Boko Haram da ke ayyukansu a Arewa maso Gabashin Najeriya ke hada kai da ’yan bindiga da ke kai hare-hare a Arewa maso Yammacin kasar.
Kamar yadda Jaridar Wall Street Journal ta ruwaito, bangarorin biyu na aiki tare da juna wajen satar mutane don neman kudin fansa daga hannun gwamnati da fararen hula.
- Buhari ya jajanta wa Amurka kan mutuwar Colin Powell
- Takardun Pandora: Peter Obi ya musanta sammacin EFCC
Jaridar ta kasar Amurka ta ruwaito cewa, Amurka ba ta ganin fashin daji a matsayin barazana a gareta.
Rahoton da sashen Hausa na BBC ya wallafa ya nado cewa, duk da rashin ganin barazanar da Amurkan ke yi, jami’anta sun jima suna sa ido kan kwamandojin ’yan bindiga da yiwuwar alakarsu da mayakan Boko haram.
Wani rahoto da jaridar ta wallafa ranar Asabar ya ce “Amurka ba ta wani damu kwarai ba da ’yan fashin daji.
“Kuma hakan na faruwa ne duk da cewa jami’an gwamnatin Amurka sun ce sun yi kutse kan wani kiran waya daga wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne da ke Arewa maso Gabashi.
“An jiyo suna bai wa ’yan bindiga a Arewa maso Yammacin kasar shawara kan garkuwa da mutane da tattaunawa don karbar kudin fansa.”
Rahoton ya kuma jaddada kiraye-kirayen da ake yi wa Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda, duk da cewa ba su da wani buri na siyasa ko addini.