✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram: Bayan shekaru manoman Borno sun koma gona

Buhari ya ba da umarnin bijiro da hanyoyin da manoma za su koma gonakinsu.

Manoma da rikicin Boko Haram ya hana yin noma tsawon shekaru a Jihar Borno, sun fara komawa gonakinsu don fara aiki.

Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya ziyarci yankunan Mulai da Dalwa a Karamar Hukumar Konduga, inda ya tattauna da jami’an tsaro don ganin manoma sun dawo gonakinsu da yin noma.

  1. DSS ta saki mawakin da ya yi wakar batanci a Kano
  2. ECOWAS ta sanar da lokacin fara amfani da kudin bai-daya

“Dole ne mu karfafa wa kanmu guiwa, ba za mu zauna babu abin da za mu ci ba. Zan samar wa kaina gona a wannan yankin, inda zan rika zuwa a ranakun hutu,” a cewar Zulum a yayin ziyarar ta ranar Lahadi.

Wannan na zuwa ne bayan umarnin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ranar Alhamis cewa jami’an tsaro su dakile ayyukan Boko Haram.

Buhari, yayin ziyararsa ta kwana daya a Borno ya ce, “Na umarci Kwamandan ‘Operation Hadin Kai’ da sauran jami’an tsaro da su yi aiki tare da gwamnatin jihar don ganin manoma sun koma noma a gonakinsu, masunta kuma su koma kamun kifi”.

Kazalika, Gwamna Zulum, ya ziyarci garin Ngwom a Karamar Hukumar Mafa, inda ya sake tattaunawa da jami’an tsaro gabanin ba wa manoma damar komawa gonakinsu.

Sannan, a garin Molai, Zulum ya je gane wa idonsa yadda aikin gina gidaje 500 ga ’yan gudun hijira ke tafiya.