Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, a ce ba zai taba yin shiru ba alhali kungiyar Boko Haram na ci gaba da kashe mutanen jihar.
Gwamnan wanda aka kai wa hari a ranar Laraba ya ce ya yi wa Allah alkawari a ranar 29 ga watan Mayu, 2019 cewa zai kare mutanen jihar Borno, don haka ba zai ga ana kashe su ya yi shiru ba.
“Alkawari ne tsakanina da Allah. A matsayina a gwamna ba zai yiwu ba in yi shiru ana ta kashe wasu daga cikin mutum milliyan shida da ke jihar”, inji shi.
A jawabinsa ga takwarorinsa na jam’iyyar APC da suka kai masa ziyarar jaje a garin Maiduguri ranar Lahadi, Gwamna Zulum ya yi zargin zagon kasa a yaki da ta’addanci a jihar, kuma lokaci ya yi na Shugaba Buhari ya san abun da ke faruwa.
“Akwai zagon kasa da ba zai taba bari yaki da ta’addanci ya kare ba. Yana da kyau Shugaban Kasa ya sani.
“Mutanenmu na bakatar a samar musu da yanayin tsaro da za su iya zuwa gonakinsu domin neman abun da za su rayu da shi. Zan ci gaba da fadar cewa ya kamata sojoji su tabbatar da faruwar hakan”, inji shi.
Zulum ya koka game da yawan ‘yan gudun hijira a jihar Borno, wandanda ya ce suna bukatar komawa gidajensu domin ci gaba da harkokinsu.
“Talauci daya ne daga cikin abubuwan da ke kawo tayar da kayar baya…Muna bukatar zaman lafiya da mutanenmu za su samu abin rayuwa”, kamar yadda ya ce.
A nasa bangaren, Bagudu ya bayyana jajensu da kuma goyon bayansu ga Gwamna Zulum, domin ganin an kawo karshen ayyukan ta’addanci a jihar.