✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bokan da ke hada wa ’yan ta’adda maganin bindiga ya shiga hannu

A cewar 'yan sanda, bokan na shirya maganin ne kan farashi N60,000 don amfanin ’yan fashin daji da makamantansu.

Wani boka da ke shirya wa ’yan ta’adda maganin bindiga a Jihar Katsina, ya fada a komar ’yan sanda.

Baya ga shirya hada bindigar, bokan kan yi wa ’yan ta’addan addu’ar kariya don kada a kama su.

Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya shida wa manema labarai ranar Talata a Katsina cewa bokan da aka cafke na zaune ne a yankin Karamar Hukumar Sabuwa ta jihar.

Ya kara da cewa, sun samu nasarar damke shi ne sakamakon bayanan sirri da suka samu a kansa.

A cewarsa, bokan na shirya maganin ne kan N60,000 don amfanin ’yan fashin daji da sauran gaggan masu laifi a jihohin Katsina da Kaduna da kuma Zamfara.

Isah ya ce bokan ya amsa laifin da ake tuhumar sa, tare da cewa za su gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike.

(NAN)