Wani boka mai suna Debare ya umarci mabiyansa su kona wani mutum da yake zargin ya gan su da kan mutum biyu a Jihar Ogun.
Wanda aka yi yunkurin konawa mai suna Lateef Adeosun, an yi yunkurin kona shi ne bayan ya ga wanda ake zargin da kawunan guda biyu a wurin ibadarsa da ke unguwar.
- RA’AYI: A yi sata, a yi kisa, a yi rashin kunya sai Najeriya (1)
- Mutum 12 sun mutu a turmutsitsin wurin ibada a Indiya
Lateef ya ce, an yi yunkurin kona shi ne bayan da ya kama mutumin mai sayar da ganyanyaki da kan mutum biyu a wurin ibadarsa.
Ya ce ya yi wa bokan aikin yanke ciyawa ce a gidansa a kan zai ba shi Naira dubu, amma bayan ya gama aikin sai bai gan shi ba.
“Na yi jira na sa’o’i da dama, sai da misalin karfe 7:30 na dare, na shiga dajin da yake aiki, domin shi masanin tsirrai ne, don haka da na isa wurin sai na gan shi tare da da wani mai suna Olawale, sannan na hadu da wani mutum mai kiba, ga shi akwai duhu na hadu da wadansu yaran Debare su hudu, wadannan yara na rike da kawunan mutum biyu sababbin yanka.
Da na gan su sai na gudu. Sai Debare da Olawale suka ce da yaran su bi ni a guje. Sai suka kama ni suka kai ni wurin ibadarsu.
Suka fara dukana, daga baya suka zuba min fetur suka banka min wuta,” inji shi. Baale (Basaraken) Kori Oja, Cif Saheed Ogunsolu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ya dade yana kula da wanda abin ya shafa.
“Ni ne nake kula da Lateef kuma ni ne Baale na wannan yanki, bayan faruwar lamarin, ya kasa yin magana tsawon wata bakwai da ya fara magana, ya bayyana yadda ya ga Debare da wadansu da kawunan mutane.
Kuma ya fadi yadda yaransa suka yi masa dukan tsiya suka banka masa wuta.”
Ya ce a yanzu haka yana karbar magani, kuma ya ce, ’yan sanda daga Sashin Binciken Manyan Laifuffuka na Tarayya (FCIID), a garin Alagbon da ke Legas sun kama Ayinla, amma a makon jiya ne an sako su.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Ogun Abimbola Oyeyemi, ya ce ba ya da masaniya kan lamarin. “Ban sani ba amma babu yadda za a yi wani ya cinna wa wani wuta a sake shi, hakan ba zai yiwu ba,” inji shi.