✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Birtaniya ta gurfanar da Diezani a gaban kotu kan zargin almundahana

Ana zarginta da karbar rashawa lokacin tana Minista a Najeriya

Kasar Birtaniya ta gurfanar da tsohuwar Ministar Man Fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke a gaban kotu kan zargin rashawa lokacin da take Minista.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa ’yan sandar kasar sun ce sun maka ta a kotun ne saboda suna zargin ta karbi cin hanci a wasu kwangilolin man fetur da iskar gas.

Diezani, mai shekara 63 a duniya, na daya daga cikin kusoshi a gwamnatin tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan.

A zamanin mulkin tsohon Shugaban, Diezani ta rike mukamin Ministar Mai ta Najeriya daga 2010 zuwa 2015, sannan ta rike matsayin shugabar Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur ta Duniya (OPEC).

A cewar Shugaban Hukumar Yaki da Laifuffuka ta Birtaniya (NCA), Andy Kelly, “gurfanarwar da aka yi wa Diezani wata somin-tabi ce na wani zuzzurfan bincike na kasa da kasa da aka dade ana yi.”

Hukumar dai ta ce ana zargin Diezani da karbar akalla tsabar kudi har Fam din Ingila 100,000 da wasu motoci da hawa jirgin da ba na ’yan kasuwa ba, yin hutun kece raini ita da iyalanta da kuma yin amfani da gidaje masu yawa a birnin Landan.

An kuma zarge ta da nuku-nuku kan wasu kadarori masu tsada da ta mallaka da suka hada da kayan ɗaki da biyan kudin makarantar ‘ya’yanta da kuma wasu sarkoki da kayan ado.

Tun da ta bar mulki a shekara ta 2015, Diezani ta rika fuskantar tuhumar aikata cin hanci da rashawa.