Wani danbindigan mai suna Biliyi wanda ake yi wa lakabi da Baushe, ya gamu da ajalinsa yayin da ya zo harbar bindigarsa ta gargajiya a wani taro da sarki ke halarata a ranar Talata.
A hirar da Aminiya ta yi da Malam Surajo, daya daga cikin ’yan uwan marigayin, ya ce, lamarin ya faru ne a unguwar Gwangwazo inda Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya je bikin bude wata makaranta a yammacin ranar Talata.
“Marigayin ya je harba bindigarsa ta gargajiya ne a bisa al’ada, domin sarki zai yi jawabi, sai ta tashi da shi, a inda ta yi masa mummunan rauni, musamman a hannuwansa,” in ji Surajo.
A sakamakon haka wayewar garin Laraba ya rasu, aka kuma yi jana’izarsa da safe a Gidan Wanzamai da ke unguwar Kawon Maigari a Kano.
Wata majiya mai karfi ta ce, Sarkin Kano ya aika da sakon ta’aziyyarsa da kuma tallafin kayan abinci da abin sadaka ga iyalan marigayin a safiyar Laraba
Marigayi Billiyi Baushe, shi ne Wakilin Maitafarin Kano a Gabas, ya mutu ya bar mata uku, da’ya’ya da kuma mahaifiyarsa.