Babbar Kotun Jihar Zamfara ta yi watsi da rokon bayar da belin wani dan bindiga da aka garfanar da shi ga gabanta.
Mai Shari’a Bello Muhammad Kucheri ya yi watsi da bukatar belin ne bayan an gaufanar da dan bindigar kan zargin ta’addanci da addabar al’ummoin jihar.
Alkalin ya bayyana cewa babu hujjar ba da belin ne, bayan da lauyan wanda ake zargi, Barista Abdulfatahu Muhammad, ya nemi belin bisa dogaro da Sashe na 35 da 36 (5) na kudin tsarin mulkin Najeriya da kuma dokar hukunta manyan laifuka ta Jihar Zamfara.
Sai dai kuma, lauya mai gabatar da kara, Barista Ibrahim B. Ahmad, ya kalubalanci rokon da cewa girman laifin ya wuci a ba da belin wanda ake zargin, domin kuwa hakan zai iya yin mummunan tasari kan shari’ar.
- Tinubu ya fara biyan dalibai kuɗin tallafin karatu
- Iyayen matashin da aka harbe a zanga-zangar Kano na neman adalci
A ranar 11 ga Mayu, 2024 aka kama wanda ake zargin, Saifullahi Muhammad, kafin a fara gurfanar da shi a ranar 27 ga yuni kan zargin hadin baki, garkuwa da mutane da ayyukan fashin daji.
Ana kuma zargin sa da hannu a tattaunawa da karbar kudin fansan wani tsohon babban sakataren gwamnati a jihar, Alhaji Abubakar Bello Furfuri, wanda ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi tare da ’ya’yansa tara.
Ana zargin sa a shiga tsakanin ’yan bindigar da iyalan Furfuri wajen yin cinikin kudin fansa Naira miliyan 80, inda ya karbi kafin alkalamin miliyan 10 ya kai wa masu garkuwar.