Fadar Shugaban Kasa ta ce binciken da wani kwamitinta ke yi wa mukaddashin shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC, Ibrahim Magu, a kan kudaden da aka kwato na nuna babu wanda ya fi karfin bincike a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Wata majiya a fadar ta ce binciken na nuna yadda gwamnatin ke mayar da hankali wajen tabbatar da yin komai a fili kuma zai ba Magu dama ya wanke kansa daga zarge-zargen da ake masa.
- EFCC: An dakatar da Magu daga mukaminsa
- Hukumar DSS ta musanta kama shugaban EFCC
- Ba kama Magu aka yi ba, inji EFCC
Majiyar ta kara da cewa, “Kwamitin da ke binciken zarge-zargen kan mukaddashin shugaban hukumar ya zauna na tsawon wasu makonni.
“Saboda a tabbatar da adalci a binciken, akwai bukatar a ba Magun damar kare kansa daga wadannan manya-manyan zarge-zargen.
“A gwamnatin Muhammadu Buhari, babu, na kara fada babu wanda ya fi karfin bincike.
“Binciken na kokari ne ya tabbatar da yin komai a fili ba tare da boye-boye ba. Ga wanda yake rike da muhimmin mukami kamar na shugaban EFCC, ya kamata a ce ba shi da kashi a gindi”, inji majiyar.
To sai dai zuwa lokacin rubuta wannan rahoto masu magana da yawun shugaban kasa sun ki cewa uffan a kan batun, musamman kan zargin korar Magu.
A wani labarin kuma, kwamitin da ke binciken Magun kan zargin badakalar karkashi shugabancin Mai Shari’a Ayo Salami ya ci gaba da zamansa a ranar Talata a dakin taro na fadar shugaban kasa.
Sai dai kamar ranar litinin, an hana manema labarai shiga wurin.
Magu dai na fuskantar zarge-zargen da ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnati, Abubakar Malami ke masa da ke da nasaba da cin hanci da rashawa.
A ranar Litinin dai fadar shugaban kasa ta ce ba kama Magun aka yi ba, gayyatar sa aka yi don ya amsa tambayoyi.