✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Binciken Ganduje: Kotu ta ba shugabannin kwamiti awa 48 su sauka

Za a tsayar da albashin alkalan da Gwamna Abba ya nada su jagoranci kwamitin binciken Ganduje.

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta umarci alkalan babbar kotun  jihar, Mai Shari’a Faruk Lawal Adamu da Mai Shari’a Zuwaira Yusuf, wa’adin awa 48 su sauka daga shugabancin kwamitocin binciken da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa domin bincikar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje.

Alkalan biyu ne ke jagorantar kwamitoci biyu da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa don bincikar Gwamnatin Ganduje kan zargin karkatar da kudade da kadarorin gwamnati da kuma kwamitin bincike kan rikicin siyasa da bacewar mutane daga 2015 zuwa 2023.

Mai Shari’a Simon Amobeda, ya umarci Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Kasa (NJC) ta tsayar da alabshi da duk da sauran hakkokin alkalan biyu, muddin suka saba umarnin kotun.

Ya sanar da haka ne a lokacin da yake yanke hukuncin kan karar da Ganduje ya shigar gaban kotun.

Ya bayyana cewa Gwamna Abba ba shi da hurumin nada alkalai domin gudanar da aikin bangaren zartarwa.

Ya kuma umarci alkalan da su daina shiga aikin bangaren zartarwa da gwamnan ya ba su, alhali suna sanye da rigarva alkalanci da yanke hukunci tsakanin bangarorin da ke da sabani da juna a jihar.

“Kundin Tarin Mulki bai halasta wa wadanda ake kara, Mai Shari’a  Faruk Adamu da Mai Shari’a Zuwaira Yusuf wadanda alakan Babban Kotun Jihar Kano ne, su karbi mukamin shugabancin kwamitin bincike ba, wanda daidai yake da matsayin alkalin kotun Majiatare,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa Gwamna Abba ba shi da hurumin nada wa da kuma rantsar da alkalai domin su gudanar da aiki shugabannin kwamitocin bincike, wanda aiki ne da doka ta ba wa Kwamishinoni da ke bangaren zartarwa.

Ya ce la’akari da hukuncin da Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman ya yanke cewa hukumar EFCC da ICPC ne kaɗai za su iya bincikar tsohon gwamna, raina kotu ne da wuce gona da iri abin Gwamna Abba ya yi na neman bincikar Ganduje, alhali gwamnatin jihar ba ta daukaka kara a kai ba kuma kotun daukaka kara ba ta jingine hukuncin ba.