✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bin Manzon Allah na gaskiya

Fassarar Salihu Makera Ina godiya  ga Allah Wanda Ya aiko ManzonSa da shiriya da addinin gaskiya domin Ya rinjayar da shi a kan dukkan addinai…

Fassarar Salihu Makera

Ina godiya  ga Allah Wanda Ya aiko ManzonSa da shiriya da addinin gaskiya domin Ya rinjayar da shi a kan dukkan addinai ko da kafirai sun ki. Ina shaidawa lallai babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya a gare Shi, mulki naSa ne, kuma cikakkiyar godiya taSa ce, Yana rayawa Yana kashewa, kuma Shi ne Wanda Ya fi sanin inda ya dace Ya sanya sakonSa, Yana halitta abin da Ya so kuma Ya zabe (shi), kuma Shi Mai iko ne a kan dukkan komai. Kuma na shaida lallai Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, kuma shi abin aikowa ne a matsayin rahama ga talikai, yana mai bushara da gargadi.
Ya Ubangiji! Ka yi tsira da aminci a gare shi da alayensa da sahabbansa da wanda ya bi shi  bisa hakkin bin sa har zuwa ranar da ake kiran kowace al’umma da shugabansu.
Bayan haka, ya ku bayin Allah! Ku bi Allah da takawa a kan hakkin bin Sa, kada ku yarda ku mutu face kuna Musulmi.
Ya bayin Allah! Ina horonku da bin Annabi (SAW) amintacce, ina horonku da yin riko da shiriyarsa da hanyarsa domin ku samu yardar Allah da ladarSa da AljannarSa.
Hudubarmu ta yau tana magana ne a kan “Bin Manzon Allah na gaskiya.”
Allah Madaukaki Ya ce: “Ba mu aiko ka ba face rahama ga talikai (dukkan duniya).” Allah Ya aiko Manzo mai girma a matsayin Manzo ga dukkan duniya domin ya kasance rahama ga wanda ya yi imani da shi kuma ya yi masa biyayya a cikin rayuwarsa da mostinsa da shirunsa. Kuma ya sanya Manzon nan a matsayin mafi daukakar jagoransa (shugabansa) kuma mafi girman abin koyinsa.
Wanda sha’aninsa ya girmama (Allah) Ya fadi ta harshen AnnabinSa amintacce cewa: “Ka ce idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni sai Allah Ya so ku.” Idan muka lura da wannan kalma “ku bi ni” lura cikakkiya, za mu fahimci abin da za mu iya samu na hakikanin ma’anarta: “Ku so ni,” na nufin wanda yake nufin koyi da wani zai rika son sa, ya haifar wa kansa son wanda yake bi.
Don haka babu makawa a nuna wa Manzon Allah (SAW) so daga farko. “Suna son su kamar son Allah, wadanda suka yi imani ne mafiya tsananin so ga Allah.”
Kuma lallai masoyi mai da’a ne ga wanda yake so. Kuma daga cikin abubuwan da Manzon Allah (SAW) ya yi umarni ga al’ummarsa akwai son sa. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ku koya wa ’ya’yanku son Annabinku.” Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “Duk abin da Manzon ya zo muku da shi (ko ya ba ku umarni) to ku rike shi, kuma abin da ya hane ku a kansa to ku hanu.”
Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “Annabi ne mafi soyuwa da dacewa da girma a wurin muminai daga rayukansu.” Muhimmi dai mu fifita son Annabi (SAW) a kan son kawunanmu, sa’annan mu bi shi ta wajen koyi da shi da biyayya gare shi a cikin adoji da ibadoji, bin Manzon (SAW) ya kunshi halaye da ibadoji. Allah Madaukaki Ya ce: “Hakika abin koyi mai kyau ya kasance a gare ku a cikin koyi da Manzon Allah, ga wanda Yake fatar (rahamar) Allah da (haduwa da Shi lami lafiya) a Ranar Lahira, kuma ya ambaci (ya tuna da) Allah da yawa.”
Ubangijin Izza Ya siffanta AnnabinSa mai girma da kyawawan dabi’u madaukaka a bayan ibada, kuma Ya rinjayar da shi a kan ‘yan uwansa (Annabawa) ta wajen kyawawan halayensa da dabi’unsa ababen godewa, sai Ya ce: “Kuma lallai, hakika kana a kan halayen kirki, manya.” Manzon Allah (SAW) ya siffantu da halayen kirki ababen yabawa. Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ka bi mummunan aiki da kyakkyawa, kuma ka yi mu’amala da mutane da kyakkyawar mu’amala.”
Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai ne wadanda suka yi imani kuma suka yi aiki na kwarai, suna da Aljannar Firadausi a matsayin makoma.”
Don haka ya bayin Allah ku kyautata ibadojinku da halayenku, ku yi koyi da Manzon Allah amintacce (SAW), duk wanda ya yi masa biyayya yana tare da shi, wanda ya saba masa ba ya tare da shi.
Ya Ubangiji! Ka sanya mu daga cikin wadanda za su riski wannan Manzo kuma Annabi mafi girma a bakin tafkinsa. Babu karfi babu dabara face ga Allah.

Huduba ta Biyu:
Godiya ta tabbata ga Wanda Ya ce: “Ba mu aiko wani Manzon ba face da harshen mutanensa domin ya yi musu bayani.” Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Annabin Larabawa da Ajamawa, wanda aka aiko shi zuwa ga dukkan mutane yana mai bushara da gargadi. Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai ne, hakika, Manzo daga cikinku ya je muku. Abin da kuka wahala da shi mai nauyi ne a kansa. Mai kwadayi ne (fatar alheri) saboda ku. Ga muminai kuma mai tausayi ne, mai jin kai.” To idan sun juya, sai ka ce: “Ma’ishina Allah ne. Babu abin bautawa face Shi. A gare Shi nake dogara. Kuma Shi ne Ubangijin Al’arshi mai girma.”       
Amintacce Almustapha (SAW) ya ce: “Abin sani an aiko ni ne domin in cika kyawawan halaye.
Hakikanin bi da koyi ga Annabi (SAW) na daga cikin manyan ayyukan da Allah Madaukaki Yake bukata daga gare mu. Kuma ibadojin addinin Musulunci suna rukunai kuma a cikin kyawawan dabi’u akwai wasu halaye. Duk wanda yake nufin ya bi Manzon Allah (SAW) to ya bi shi ta wajen dacewa da ayyukansa ba da munafunci ba. Ya yi bincike kuma ya yi tambaya kan kaifiyyar yadda yake ibadojinsa (SAW) da halayensa. Misali akwai rukunan Musulunci guda biyar biyar, ana farawa da imani, sai Sallah da zakka da azumi da Hajji. Duk wanda ya saba masa wajen yin dukkan wadannan abubuwan da aka ambata, hakika ya kauce hanya, ba ya da hakkin da’awar cewa yana bin Manzon Allah (SAW). Kowane daya daga cikin al’ummar Annabi Muhammad (SAW) yana da mukami gwargwadon martabar ibadarsa. Wannan na kowa ne, akwai na kebantattu, akwai na kebanattun kebantattu. Akwai ibadar masu ibada. Kuma Musulunci yana da wasu muhimman bangarori uku, wato Musulunci da Imani da Ihsani. Kuma a wajen niyyar bi ko koyin akwai abubuwa uku.
Wadannan abubuwa uku na abin da ake neman bawa ya yi su ne Takhalli da Tahalli da Tajalli. A samu Takhalli gabanin Tahalli sai Tahalli gabanin Tajalli.
1.    Takhalli: Shi ne nisantar ababen ki ko barin aikata alfasha da ababen ki da zanubi da duk abin da Allah Ya hana da abin da ManzonSa (SAW) ya hana. Kamar karya da algush da sata da zina da munafunci da shan giya da annamimanci da girman kai da jiji-da-kai da alfahari da riya da fasikanci da zalunci da cin riba da cin dukiyar marayu da sauransu. Babu makawa kowane Musulmi ko mumini ko muhsini ya ciru daga gare su domin ya samu cimma manufar yin biyayya da koyi da Manzon Allah (SAW).
2.    Tahalli: Shi ne ya zamo tambarin Musulmi, mumini, muhsini, ya kasance ibadoji da kyawawan halaye na Manzon Allah (SAW). Daga cikinsu akwai yin sallolin farillai da na sunnoni a kan lokacinsu. Kuma ya tsayu da halaye ababen godiya. Kada ya kyautata ibadarsa, sannan ya munana halayensa.
Wani ya rera cewa:
“Ilimi da adabu da wadata ba su da amfani,   Matukar mai su bai fuskanci Ubanjgijinsa da kyawawan halaye ba.”
Adonsa ya zamo takawa ga Allah da kyautata ibada gare Shi, ta wajen Sallah da hakuri da kyauta da tausasawa da sakin fuska da tsoron Allah da sauransu.
3.    Tajalli: Shi ne mutum Musulmi, mumini, muhsini, ya tsaya a matsayin bawan Allah, ya kasance wanda yake kangewa daga aikata laifuffuka, ya zamo al’amarinsa yana dacewa da umarnin Allah, ya zamo duk abin da zai darsu a zuciyarsa shi ne Manzon Allah (SAW), yaya ya yi kaza da kaza. “Ku yi Sallah kamar yadda kuka ina yin Sallah.” Wannan na nuna cewa Manzon Allah (SAW) yana nufin: “Ku ci abinci kamar yadda kuka ga ina ci, ku sanya sutura kamar yadda kuka ga ina sanyawa…” haka a ayyukan ibada da siyasa, don haka siyasa ma tana cikin mafiya alherin abin da za a kwaikwaya daga Manzon Allah (SAW).
Allah Madaukaki Ya fadi a cikin wani Hadisin kudisi cewa:  “Bawa bai gushe ba yana kusantaTa da nafilfili har sai Na so shi. Idan Na so shi, sai in kasance jinsa da yake ji da shi, da ganinsa da yake gani da shi da hannunsa da yake damka da shi da kafarsa da yake tafiya da ita. Idan ya roke Ni, wallahi sai na ba shi, kuma idan ya nemi tsariNa, wallahi zan tsare shi…” har zuwa karshen Hadisin.
Duk wanda yake son kaiwa ga Tajalli ba makawa ya bi ta kan Takhalli da Tahalli.
Ya ku bayin Allah! Ku sanya hakkin bi da koyi da Manzon Allah (SAW) ya zamo mabudi ga kofar wannan shekara da muke ciki.
Lallai Allah Yana umarni da adalci da kyautatawa da ba ma’abucin zumunta hakkinsa, kuma Yana hani daga alfasha da abin ki da zalunci. Yana yi muku wa’azi tsammaninku kuna tunawa.